Sojoji sun tare shanun sata 154, sun damke miyagu 44 a Zamfara

Sojoji sun tare shanun sata 154, sun damke miyagu 44 a Zamfara

  • Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Hadarin daji ta samo shanu 154, rakumi 1 da rago daya da miyagu suka sace
  • Mataimakin shugaban rundunar a jihar Zamfara, Abubakar Abdulkadir, ya ce sun tare miyagun ne a manyan motoci 12 dake tunkarar Gusau
  • Rundunar ta mika dabbobin ga gwamnatin jihar Zamfara tare da damke mutum 44 da take zargi da satar dabbobin

Rundunar Operation Hadarin Daji, ta tare motoci manya 12 dankare da shanu 154 tare da kame miyagu 44 a jihar Zamfara, Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Mataimakin kwamandan rundunar, Air Commander Abubakar Abdulkadir, ya sanar da hakan a Gusau a ranar Juma'a yayin mika shanun satan ga gwamnatin jihar Zamfara.

Abdulkadir ya ce an kama wadanda ake zargin ne yayin da suke tafe da shanu 154, rakumi daya da kuma rago daya a manyan motoci kan hanyarsu ta zuwa Gusau.

KU KARANTA: Tsaro: Hankalina yafi kwanciya a Maiduguri fiye da Abuja, Sanata Ndume

Sojoji sun tare shanun sata 154, sun damke miyagu 44 a Zamfara
Sojoji sun tare shanun sata 154, sun damke miyagu 44 a Zamfara. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon bikin soja mace, ana kada ganga tare da mika mata takobi

Ya ce wadanda ake zargin an kama su ne jim kadan bayan sun bar kasuwar Yartasha wuraren yankunan Magami da Jangeme a karamar hukumar Gusau.

Kamar yadda yace, jami'an rundunar Operation Lafiya Dole zasu cigaba da tsananta yaki da ayyukan 'yan ta'adda a yankin arewa maso yamma, Daily Nigerian ta ruwaito.

"Ba zamu gaza ba wurin bada kariya ga rayuka da kadarorin 'yan kasa ba," Abdulkadir yace.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, sakataren gwamnatin jihar na kwamitin samo dabbobin sata, Bashar Mailafiya, ya ce kwamitin ya karba shanu 154, rakumi 1 da rago daya daga sojoji.

Mai lafiya wanda ya jinjinawa kokarin sojojin ya ce kwamitin zai tabbatar da ya nemi masu dabbobin kuma an mika musu.

A wani labari na daban, kungiyar matasan arewa (AYA) ta ce ta shirya fito na fito da duk mai barazana ga shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da yace yana samun barazanar mutuwa saboda manyan da ya addaba a kan rashawa.

Marasa rinjaye a majalisar wakilai a ranar Alhamis sun yi kira ga gwamnatin tarayya da kada su yi watsi da wannan barazanar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel