2023: Manyan matsaloli 7 dake barazanar hargitsa APC a jihar Kano

2023: Manyan matsaloli 7 dake barazanar hargitsa APC a jihar Kano

Sauran shekaru biyu zabe amma akwai manyan kalubale dake kokarin tarwatsa jam'iyyar APC a jihar Kano, babbar cibiyar kasuwancin arewa kuma jihar da jam'iyyar ke takama da kuri'unta.

Manyan matsalolin da suka samu zama a babbar cibiyar kasuwancin arewan zasu iya zama kalubale ga jam'iyyar a fadin Najeriya saboda yawan kuri'un da ake samu daga jihar.

Matsalolin sun fara bayyana ne a ranar Laraba biyo bayan sanarwar dakatarwa da aka yi wa dan majalisa mai wakiltar birnin Kano a majalisar wakilai, Sha'aban Ibrahim Sharada.

KU KARANTA: Hotunan cikin katafaren gidajen Mark Zuckerberg masu darajar N131b

2023: Manyan matsaloli 7 dake barazanar hargitsa APC a jihar Kano
2023: Manyan matsaloli 7 dake barazanar hargitsa APC a jihar Kano. Hoto daga @Thecable
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke likita a Magama, jihar Neja

Sharada/ Ganduje

Sharada, tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari sun kasance basu jituwa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma shugabannin APC na Kano.

Abdullahi Umar, shugaban jam'iyyar a gundumarsa ya ce an dakatar da Sharada ne saboda zarginsa da ake da ayyukan da suka sabawa jam'iyya da kuma bata sunan gwamnan jihar.

Gumurzun neman shugabancin jam'iyya

Daga cikin manyan matsalolin APC a Kano akwai gumurzun kaunar shugabancin jam'iyyar tsakanin shugaban rikon kwarya, Abdullahi Abbas da kuma tsohon shugaban CPC, Ahmadu Haruna Danzago.

Bara’u Jibrin da Sule-Garo/Gawuna

Wata matsalar ita ce wacce ke tsakanin Sanata Barau Jibrin da kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule-Garo.

Duk da yankinsu daya, kowannensu yana da burin juya siyasar yankin, hakan ke kawo baraka tsakaninsu tunda kowanne yana amfani da 'yan daba mabiyansa.

Sanata Jibrin na da burin gadon Ganduje a 2023 yayin da Sule-Garo ke son zaman mataimakin a 2023 a tikitin Nasiru Yusuf Gawuna.

Shekarau da Ganduje

Duk Da Gawuna yayi aiki da gwamnonin Kano uku tun bayan dawowar damokaradiyya a 1999, ya fito haske ne a yayin mulkin Malam Ibrahim Shekarau.

Majiyoyi daga bangaren Shekarau sun nuna cewa babu jituwa tsakanin bangaren Ganduje da na tsohon gwamnan, domin suna zarginsa da rashin adalci garesu duk da rawar da suka taka yayin zarcewarsa a 2019.

Kungiyoyin goyon bayan Buhari

A wata budaddiyar wasika da kwamitin daukaka kara na rijista na APC wanda ya samu sa hannun Shehu Dalhatu na kungiyar goyon bayan Buhari, sun koka da rashin adalcin da aka bayyana yayin sabunta rijistar 'yan jam'iyyar.

Amma a wani martani da aka yi wa kungiyar, manyan masu mukami a gwamnatin jihar sun ce kungiyar tana aiki ne da abokan hamayya domin zagon kasa ga jam'iyyar.

APC Akida ta Kwamanda

A cikin kwanakin nan ne wani mai goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Kano, Abdulmajid Danbiliki Kwamanda, ya kirkiro wani bangaren APC kuma ya sa mata suna APC Akida, lamarin da yasa aka kore shi daga jam'iyyar.

Sabbin 'yan jam'iyya masu fatan samun tikitin takara a 2023

Sakamakon gangamin jam'iyyar da aka yi a Kano wanda hakan yasa tsoffin 'yan takarar kujerar gwamnan jihar uku daga wasu jam'iyyu suka koma APC, kokarin samun tikitin takarar gwamna a 2023 karkashin jam'iyyar zai zama gagarumin aiki

A wani labari na daban, rundunar Operation Hadarin Daji, ta tare motoci manya 12 dankare da shanu 154 tare da kame miyagu 44 a jihar Zamfara, Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Mataimakin kwamandan rundunar, Air Commander Abubakar Abdulkadir, ya sanar da hakan a Gusau a ranar Juma'a yayin mika shanun satan ga gwamnatin jihar Zamfara.

Abdulkadir ya ce an kama wadanda ake zargin ne yayin da suke tafe da shanu 154, rakumi daya da kuma rago daya a manyan motoci kan hanyarsu ta zuwa Gusau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng