ASUU ta yi Allah wadai da korar malaman jami’a da gwamnatin Kaduna ta yi

ASUU ta yi Allah wadai da korar malaman jami’a da gwamnatin Kaduna ta yi

-An kori ma’aikata 18 saboda shiga cikin yajin aikin gargadi na kwana biyar da kungiyar kwadagon Najeriya, ta kira a jihar, tsakanin 17 zuwa 19 ga watan Mayu

-Mista Adamu ya ce, kokarin korar ma'aikatan 18 ba bisa ka'ida ba ya sabawa yarjejeniyar fahimtar juna, MoU, da aka sanya wa hannu

-Yarjejeniyar ta bayyana karara cewa babu wani ma'aikaci da za a ci zarafinsa saboda ya shiga yajin aikin

Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, reshen Jami’ar Jihar Kaduna, KASU, ta nuna rashin amincewarta da korar malamai 16 da ma’aikatan jami’ar guda biyu wadanda ba malamai ne ba da gwamnatin jihar ta yi.

An kori ma’aikatan 18 saboda shiga cikin yajin aikin gargadi na kwana biyar da kungiyar kwadagon Najeriya, ta kira a jihar, tsakanin 17 zuwa 19 ga watan Mayu.

Shugaban kungiyar kwadagon a jihar, Peter Adamu, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Kaduna ranar Litinin, ya bayyana matakin a matsayin haramtacce, rahoton Daily Nigerian.

Mista Adamu ya ce, kokarin korar ma'aikatan 18 ba bisa ka'ida ba ya sabawa yarjejeniyar fahimtar juna, MoU, da aka sanya wa hannu tsakanin kungiyar kwadago da Gwamnatin Jihar Kaduna, a ranar 20 ga Mayun.

Ya ce yarjejeniyar ta bayyana karara cewa babu wani ma'aikaci da za a ci zarafinsa saboda ya shiga yajin aikin.

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

ASUU ta yi Allah wadai da korar malaman jami’a da gwamnatin Kaduna ta yi
ASUU ta yi Allah wadai da korar malaman jami’a da gwamnatin Kaduna ta yi Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU DUBA: Buhari fa ko amfani da wayar Andriod bai iya ba ballantana Tuwita, Fayose

Mista Adamu ya kara da cewa, wannan korar “karya doka ce” kan yarjejeniyar fahimtar juna da Gwamnatin Jihar Kadunan ta shiga.

Ya bayyana cewa Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammad Tanko ne ya sanar da korar a lokacin taro na 16 na jami’ar wanda aka gudanar a ranar 2 ga Yuni.

“Shaidar wannan korar da jami’ar ta dauka na cikin takarda mai lamba (KASU / REG / 061 / VOL 1/446) daga shugabanin jami’ar har zuwa Gwamna Nasir El-Rufai, ta hannun Kwamishinan Ilimi mai dauke da kwanan wata 20 ga watan Mayu.

“Amma, ma’aikatan guda 18 da abin ya shafa ba su samu amsa ba kuma ba su fuskanci wani kwamitin ladaftarwa ba, kamar yadda shugabannin jami’ar suka yi ikirari a cikin takardar.

"Da'awar karya ce kuma ba ta da tushe ba tare da wata shaidar da za a nuna ba," inji shi.

Mista Adamu ya kara da cewa wasikar ta Shugaban Jami’ar ta kuma umarci ofishin Akanta Janar na Jihar Kaduna, da ta dakatar da tura kudaden harajin kungiyar kwadagon.

Wannan, a cewarsa, ya sabawa dokar Kungiyoyin Kwadago ( da aka yi wa kwaskwarima) Doka Mai Lamba 17 na 2005, wanda za a cire kudaden tallafin ba tare da sanar da ma’aikaci ba.

“Duk da tanadin dokokin, gwamnatin Jihar Kaduna da kuma KASU ba bisa ka’ida ba, sun shirya tare da korar ma’aikata da kuma dakatar da biyan kudaden shigan kungiya.

"An yi wannan ba tare da bin Dokokin Jami'ar da kuma dokokin kwadago na kasa da na duniya ba," inji shi.

Shugaban ya yi tir da matakin korar kuma ya yi kira ga shugabannin jami’ar da su janye matakin da suka daukan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa Shugaban Jami’ar a cikin wasikar zuwa ga El-Rufai, ya gano malamai 16 da kuma wadansu ma’aikatan jami’ar wadanda suka shiga cikin yajin aikin NLC.

Mista Tanko ya bayyana a cikin wasikar cewa an tura sunayen ma'aikatan da abin ya shafa zuwa ofishin Shugaban Ma'aikata tare da cike fom din barin aiki, domin dakatar da albashinsu daga ranar 20 ga watan Mayu.

Ya bayyana cewa an bi tsarin gudanar da aiki bisa dogaro da Dokar Jami'a da Yanayin Aiki na Ma’aikata, wanda ya nuna karara matakan ladaftarwar da za a dauka.

Yace: “Hanyoyin aiwatar da ladabtarwa a kan shari’o’in da aka tabbatar na mummunan rashin da’a kamar yadda suke kunshe yana haifar da kora daga aiki kai tsaye, wanda ya hada da gabatar da tuhuma ga ma’aikatan da abin ya shafa.

“Bayan ma’aikatan da abin ya shafa sun amsa tuhuma kan zargin da aka yi musu, ma’aikatan da abin ya shafa za su bayyana a gaban Kwamitin da’a."

“Kwamitin ladabtarwa ya gabatar da rahoton ga Shugaban Jami’ar kuma ya amince da shawarwarin da kwamitin ya bayar a madadin Majalisar Gudanarwa, kuma Magatakarda ya aiwatar da shawarwarin."

Kun ji cewa hukumar gudanarwan Jami'ar Jihar Kaduna (KASU) ta bayyana cewa, ta dakatar da ayyukan karatu na daliban digiri na farko a makarantar zuwa wani lokacin da ba ta ayyana ba.

Sai dai, hukumar gudanarwar ta bayyana wasu fannonin karatun da ba ta dakatar dasu ba, kamar yadda yazo a sanarwar da ta fitar a yau Talata 8 ga watan Yunin 2021.

Cikin wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samu, hukumar gudanarwar ta KASU ta fidda sanarwar mai nuni da dakatar da ayyukan karatu, amma ta umarci ma'aikatan makarantar da su ci gaba da zuwa aiki kamar yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng