Matasan arewa, 'yan majalisa sun bukaci daukan mataki kan barazanar sheke shugaban EFCC

Matasan arewa, 'yan majalisa sun bukaci daukan mataki kan barazanar sheke shugaban EFCC

  • Kungiyar matasan arewa (AYA) ta ce ta shirya gaba da gaba da duk wanda zai yi wa shugaban EFCC barazanar kisa
  • Marasa rinjayen majalisar wakilai sun ce ya zama dole a bincika lamarin kuma FG ta dauka mataki a kai
  • Kamar yadda marasa rinjayen suka bayyana, duk abinda ya faru da Bawa tare da kare masu cin rashawa laifin FG ne

Kungiyar matasan arewa (AYA) ta ce ta shirya fito na fito da duk mai barazana ga shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da yace yana samun barazanar mutuwa saboda manyan da ya addaba a kan rashawa.

Marasa rinjayen majalisa sun yi magana

Marasa rinjaye a majalisar wakilai a ranar Alhamis sun yi kira ga gwamnatin tarayya da kada su yi watsi da wannan barazanar, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: 'Yanin tarayya da bindiga sun sheke mutum 1, sun yi garkuwa da 'yan Chaina 2 a Taraba

Matasan arewa, 'yan majalisa sun bukci daukan mataki kan barazanar sheke shugaban EFCC
Matasan arewa, 'yan majalisa sun bukci daukan mataki kan barazanar sheke shugaban EFCC. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Duba dankareriyar mota kirar Roll Royce Cullinan Suv ta N100m da tsohon sanata ya siya

AYA sun yi taron manema labarai

Awani taron manema labarai, mai magana da yawun AYA, Mohammed Salihu Danlami ya ce bai kamata a hana Bawa abun arzikin da ya fara ba, Daily Trust ta ruwaito.

"Duk wani hari ko barazana kan shugaban, barazana ce garemu kuma dole ne mu bincika sannan hukuma ta dauka mataki," yace.

“Kada a zuba ido ana kallon wannan lamari. A matsayinmu na matasa a kasar nan, mun nuna goyon baya ga shugaban tun lokacin da aka nada shi kuma a shirye muke mu kasance a bayansa har sai ya cimma nasara."

Kada a bar wannan barazanar haka

Bangaren marasa rinjaye na majalisar wakilai, sun fitar da takarda wacce shugabansu Ndudi Elumelu yasa hannu kuma ya bayyana wannan barazana da abun damuwa.

Elumelu ya ce kokarin kare miyagun jami'an gwamnati masu cin rashawa da kuma duk abinda zai faru da shugaban EFCC za a daura alhakin ne kan gwamnatin tarayya.

"Muna kira ga shugaban EFCC da ya fito fili kuma ya bayyana mana sunayen masu yi masa barazana.

"Muna bukatar a gaggauta fara bincike saboda barazanar da aka yi ga rayuwar shugaban EFCC ba za ta tafi a haka ba," majalisar ta bukata.

A wani labari na daban, Francis Atuche, tsohon manajan daraktan tsohon bankin PHB Plc, ya samu hukuncin shekaru shida a gidan yari kan damfarar makuden kudade har N25.7 biliyan.

Mai shari'a Lateefat Okunnu ta babbar kotun dake Ikeja a ranar Laraba, 16 ga watan Yuni ta hada da tsohon jami'in kudi na bankin, Ugo Anyanwu shekaru shida a kan laifin, Premium Times ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa alkalin ta sallama tare da wanke matar Atuche mai suna Elizabeth. A yayin yankewa su biyun hukunci, mai shari'ar ta ce EFCC ta tabbatar da kokenta kuma babu shakka hakan ya faru sama da shekaru 10 da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel