Tsaro: Hankalina yafi kwanciya a Maiduguri fiye da Abuja, Sanata Ndume

Tsaro: Hankalina yafi kwanciya a Maiduguri fiye da Abuja, Sanata Ndume

  • Sanata Ali Ndume ya ce yafi samun natsuwa idan yana garin Maiduguri fiye da Abuja
  • Shugaban kwamitin sojoji a majalisar dattawa yace tsaro ya inganta a garin Maiduguri
  • Ya kwarzanta jarumtar shugaba Buhari da yayi yawon sa'o'i shida a cikin jihar Borno

Sanata Ali Ndume ya ce yafi samun natsuwa da kwanciyar hankali idan yana Maiduguri, babban birnin jihar Borno fiye da idan yana garin Abuja, babban birnin kasar Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Boko Haram ta dinga kai farmaki Maiduguri da garuruwan dake da kusanci da nan amma lokacin da Ndume ya zanta da Channels TV a shirin siyasarmu a yau ta ranar Alhamis, shugaban kwamitin sojin yace tsaro ya inganta a babban birnin Borno.

KU KARANTA: Duba dankareriyar mota kirar Roll Royce Cullinan Suv ta N100m da tsohon sanata ya siya

Tsaro: Hankalina yafi kwanciya a Maiduguri fiye da Abuja, Sanata Ndume
Tsaro: Hankalina yafi kwanciya a Maiduguri fiye da Abuja, Sanata Ndume. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Damfarar N25.7b: Kotu ta yankewa tsohon Manajan fitaccen banki shekaru 12 a gidan yari

Hankalina yafi kwanciya a Maiduguri

"Ina zama a Abuja da Maiduguri. Amma matukar ina Maiduguri, ina jin kwanciyar hankali fiye da Abuja saboda wani zai iya buga min kofa kuma ya saka min bindiga. A Maiduguri kuwa babu wannan tsoron."

"A wajen Maiduguri ne ake samun 'yan ta'adda kuma dama matsorata ne. Sai dai su yi barna kuma su tsere.

“A kowacce al'umma, ba a iya hana ta'addanci. A Amurka, an samu inda aka dinga harbi a makaranta. A nan muna da sanannun 'yan ta'adda kuma sojoji suna yakarsu."

Sanata Ndume, wanda a kodayaushe yake kira ga gwamnati da ta kara zuba kudi a fannin tsaro, ya ce tsaro yana inganta da jajircewar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanata Ndume ya kwarzanta jarumtar Buhari

Sanatan ya kwatanta ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ziyarar karfafa guiwa ga dakarun sojin dake filin daga.

"Shugaban kasan yayi yawon sa'o'i shida - Na gaji. Ya shigo wurin karfe 10 kuma muka duba ayyuka masu yawa har zuwa karfe hudu na yamma kafin ya tafi," yace yayin kwarzanta jarumtar shugaban kasan.

A wani labari na daban, Ofishin hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa (EFCC) ta fara bincike kan zargin wasu mutum uku da ake da hada kai wurin cuta tare da buga kudin jabu.

Wadanda ake zargin sun hada da Sylvanus Ireka Ifechukwu, Patrick Chima ibiam da Ajimijere Mathias Adegbenro, Channels TV ta ruwaito.

'Yan sanda na bangaren bincike na musamman dake hedkwatar hukumar ta Obalende, jihar Legas sun yi kamen a ranar 30 ga watan Afirilun 2021 kuma suka mika su gaban EFCC domin cigaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng