Sojoji sun halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a kakkabar makonni 2 da suka yi a kudu

Sojoji sun halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a kakkabar makonni 2 da suka yi a kudu

  • Dakarun sojin kasar nan sun yi ayyukan kakkabar masu laifi a yankin kudancin kasar nan
  • Sun samu nasarar sheke 'yan ta'adda masu tarin yawa a yankin kudu maso gabas da kudu kudu
  • 'Yan ta'addan IPOB da takwarorinsu na ESN sun addabi yankin kudu inda suke kaiwa jami'ai farmaki

'Yan ta'addan da ba a san yawansu sun halaka sakamakon ayyukan kakkabar 'yan ta'adda da sojoji suka yi a yankin kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan a cikin makonni biyu da suka gabata.

A ranar Alhamis ne hedkwatar tsaro tace 'yan ta'adda masu yawa dake da alaka da IPOB da ESN sun bakunci lahira, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kurmushe gidan dan majalisa a Imo, sun sheke maigadi

Sojoji sun halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a kakkabar makonni 2 da suka yi a kudu
Sojoji sun halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a kakkabar makonni 2 da suka yi a kudu. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi garkuwa da 'yan Chaina 2 a Taraba

Halaka 'yan ta'addan ya zo ne a samame daban-daban tsakanin 3 ga watan Yuni zuwa 16 ga watan Yuni inda aka dinga dakile miyagun ayyukan IPOB da ESN.

Samame

A ranar 4 ga watan Yuni, jami'ai sun kai samame wata maboyar 'yan ta'adda dake Ukpong a karamar hukumar Obot Akara dake jihar Akwa Ibom.

Duk a ranar daya, dakarun sojin sun yi luguden wuta kan wasu 'yan IPOB da ESN wadanda suka kai hari garin Okposi dake karamar hukumar Ohaozara ta jihar Ebonyi.

A ranar 5 ga watan Yuni, sojoji sun yi wa wasu 'yan IPOB luguden wuta wadanda suka tare masu wucewa ta babban hanyar Igbo-Ekiti zuwa Nsukka dake jihar Enugu, Daily Trust ta ruwaito.

A wannan ranar, dakarun sun bi wasu 'yan ta'adda wadanda suka lalata dogo a titin Nkwubor dake karamar hukumar Enugu ta gabas, Onyeuko yace.

A wani labari na daban, Francis Atuche, tsohon manajan daraktan tsohon bankin PHB Plc, ya samu hukuncin shekaru shida a gidan yari kan damfarar makuden kudade har N25.7 biliyan.

Mai shari'a Lateefat Okunnu ta babbar kotun dake Ikeja a ranar Laraba, 16 ga watan Yuni ta hada da tsohon jami'in kudi na bankin, Ugo Anyanwu shekaru shida a kan laifin, Premium Times ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa alkalin ta sallama tare da wanke matar Atuche mai suna Elizabeth. A yayin yankewa su biyun hukunci, mai shari'ar ta ce EFCC ta tabbatar da kokenta kuma babu shakka hakan ya faru sama da shekaru 10 da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel