Labari mai dadi yayin da 'yan gudun hijira a Taraba suka koma gidaje da gonakinsu

Labari mai dadi yayin da 'yan gudun hijira a Taraba suka koma gidaje da gonakinsu

  • Bayan shafe watanni a sansanonin ‘yan gudun hijira,‘yan gudun hijira a Taraba na komawa gida don fara ayyukan noma
  • Zaki David Gbaa, shugaban majalisar sarakunan gargajiya a jihar, ya ce ci gaban zai hana yunwa da ke kara kamari
  • David Gbaa ya nuna godiya ga gwamnan jihar, Darius Ishaku, kan amincewa da komawar 'yan gudun hijirar da kuma samar da yanayin da zai ba da damar yin hakan

Wasu 'Yan Gudun Hijira (IDPs) a jihar Taraba na komawa yankunansu biyo bayan umarnin da gwamnan jihar, Darius Ishaku ya bayar.

Shugaban majalisar sarakunan gargajiyan Tiv na jihar Taraba kuma Ter Tiv Bali, Zaki David Gbaa, ya tabbatar da ci gaban, jaridar The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Shahararren sanatan PDP ya kayar da EFCC a kotu, ya yi nasara a karar da aka shigar

Labari mai dadi yayin da 'yan gudun hijira a Taraba suka koma gidaje da gonakinsu
Gwamnan jihar Taraba, Darius Dickson Ishaku Hoto: Governor Darius Dickson Ishaku
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa David Gbaa ya kara da cewa shugaban karamar hukumar Bali, Prince Musa Mahmud, zai taimaka wajen dawo da duk wadanda suka rasa muhallansu a karamar hukumar zuwa gidajensu.

Basaraken ya lura cewa an aika wasika kan hakan ga dukkan masu rike da sarautun gargajiya a karamar hukumar, ya kara da cewa mutane suna komawa gonakinsu sosai, jaridar Nigerian Tribune ta kuma ruwaito.

Zaman lafiya ya dawo, yunwa ya kau

David Gbaa ya gode wa Gwamna Ishaku saboda tabbatar da dawowar zaman lafiya ga garuruwan da ke cikin rikici.

Kalaman nasa:

"Wannan ci gaban zai dawo da zaman lafiya ga garuruwanmu kuma zai magance yunwa a yanzu da mutane ke komawa gonakinsu."

KU KARANTA KUMA: Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya bayyana matsayarsa game da tsayawa takarar siyasa a Najeriya

Wasu daga cikin yan gudun hijirar sun kuma yabawa Ishaku saboda samar musu da yanayin da zai basu damar komawa gidajen su bayan sun kwashe watanni a sansanin.

A kyalle yan Nigeria sun fara mallakar AK 47, Gwamna Ishaku

A wani labarin, Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishiaku a ranar Laraba, ya roki gwamnatin tarayya da sahalewa ko wane dan kasa lasisin rike bindiga don su kare kansu, ya na mai cewa jami'an tsaro sun gaza.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da shugabannin kananan hukumomi 15 na jihar suka kai masa ziyarar ta'aziyyar daya daga cikin abokan aikin su da yan bindiga suka sace kuma suka kashe shi daga baya.

Ya kuma janjantawa iyalan wanda suka rasa rayukan su sanadiyar rashin tsaro da ya addabi sassan kasar nan yayin da yake shawartar sauran yan Najeriya da su zama masu sanya ido.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng