A kyalle yan Nigeria sun fara mallakar AK 47, Gwamna Ishaku

A kyalle yan Nigeria sun fara mallakar AK 47, Gwamna Ishaku

- Gwamna Darius na Jihar Taraba ya bukaci a bar yan kasa su mallaki bindiga matukar baza a chanja salo ba

- Gwamnan ya ce matukar gwamnati ba zata iya kare yan kasa ba to ta basu damar kare kan su

- Gwamnan ya bukaci mutane su ci gaba da sanya ido sakamakon irin rashin tsaron da ake fama da shi

Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishiaku a ranar Laraba, ya roki gwamnatin tarayya da sahalewa ko wane dan kasa lasisin rike bindiga don su kare kansu, ya na mai cewa jami'an tsaro sun gaza.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da shugabannin kananan hukumomi 15 na jihar suka kai masa ziyarar ta'aziyyar daya daga cikin abokan aikin su da yan bindiga suka sace kuma suka kashe shi daga baya.

A kyalle yan Nigeria sun fara mallakar AK 47, Gwamna Ishaku
A kyalle yan Nigeria sun fara mallakar AK 47, Gwamna Ishaku
Asali: Twitter

Ya ce, "idan kuna ta yin abu daya kullum kuma ba a samu nasara to ya kamata ku koma wajen wanda zai baku wata shawarar daban da zata yi aiki.

"Bai kamata ayi ta yin abu daya ba daidai ba. Kuma idan baza mu iya tsare rayukan jama'a ba to mu bari su siyi AK47 (bindiga).

Idan aka sahalewa kowa AK47 (bindiga), na rantse....babu wanda zai shigo gidan ka kuma ko da mutum ya shigo ma gida, ya rage kuma tsakanin kai da shi wa yafi sauri tsakani.

"Amma a yanayi irin wanda za a ce mu jira wani jami'in tsaro ya tsare mu, kuma an kasa samun nasara sai dai mu zauna muna jiran ranar da abu zai same mu; ni ban yadda da wannan ba."

Ya kuma janjantawa iyalan wanda suka rasa rayukan su sanadiyar rashin tsaro da ya addabi sassan kasar nan yayin da yake shawartar sauran yan Najeriya da su zama masu sanya ido.

Asali: Legit.ng

Online view pixel