Bawa Ya Bayyana Yadda EFCC Zata Bankado Wadanda Ke Hana Najeriya Ci Gaba

Bawa Ya Bayyana Yadda EFCC Zata Bankado Wadanda Ke Hana Najeriya Ci Gaba

  • Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa, yana nan daram, kuma sai ya bankado masu hana ruwa gudu a Najeriya
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, yana mai jaddada kwarin gwiwar aikinsa
  • Ya ce hukumar tana hada kai da duka masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da an kai Najeriya ga tudun na tsira

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ya ce hukumar za ta bakado wadanda ke dakile ci gaban Najeriya, TheCable ta ruwaito.

Da yake jawabi a taron manema labarai na gidan gwamnatin da aka yi a Abuja ranar Alhamis, Bawa ya ce EFCC ta dukufa wajen tabbatar da cewa Najeriya ta kubuta daga dukkan nau'ikan laifuka da suka shafi kudi da tattalin arziki.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Isa Borno, Ya Bukaci Sojoji Su Kara Daura Damara

Bawa: EFCC zata kwamuso wadanda ke hana Najeriya ci gaba
Shugaban hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa | Hoto: channelstv.com
Asali: Facebook

Ya ce hukumar na da “kwarin gwiwar ma’aikata da goyon baya daga kowane mai ruwa da tsaki a cikin gida da waje don cimma manufar Najeriya na zama ba tare da aikata nau’ikan laifukan tattalin arziki da na kudi ba”.

“Najeriya ce kadai kasar da muke da ita. Mu ne wadanda za mu kiyaye ta kuma ba shakka, muna bukatar goyon bayan wadanda suke gida da kuma kasashen waje,” inji shi.

"Don Allah kar ku tsallaka layin nan kuma ku tuna cewa idan ba ku tare damu mu a kokarin kai Najeriya tudun na tsira, EFCC za ta bankado ku a ko'ina, kowane lokaci."

Yayin da yake magana a cikin shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin din Channels, a ranar Talata, shugaban na EFCC ya ce yana ta samun barazanar kisa tun lokacin da ya zama shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

A watan Fabrairun 2021, an nada Bawa a matsayin shugaban EFCC don maye gurbin Ibrahim Magu, tsohon shugaban riko na hukumar yaki da rashawa.

KU KARANTA: An kame wani Fasto da ya kashe matarsa, ya binne gawar a kusa da cocinsa

EFCC Ta Bayyana Yadda Ake Sace Kudin Najeriya da Bitcoin, Ta Kwato Miliyoyi

A wani labarin, Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta kwato kimanin dala miliyan 20 da barayi a yanar gizo suka wawure.

Mista Bawa, ya bayyana haka ne yayin shirin ‘Sunrise Daily’ na Channels Tv, ya kara da cewa an adana kudaden a cikin asusun yanar gizo na hukumar EFCC, Punch ta ruwaito.

Babban Bankin Najeriya a watan Fabrairun 2021 ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kudi su gano mutane da kungiyoyin da ke musayar kudin Intanet tare da rufe dukkan wadannan asusun.

Hakanan ya bayyana cewa ma'amala da musayar kudade da biyan kudi ta hanyar kudaden intanet haramun ne a kasar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel