Baba Oyoyo: Muhimman Jawabai 11 da Shugaba Buhari Ya Yi a Ziyararsa Ta Borno

Baba Oyoyo: Muhimman Jawabai 11 da Shugaba Buhari Ya Yi a Ziyararsa Ta Borno

A ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, shugaba Buhari ya kai ziyara jihar Borno, inda ya tattauna da jami'an sojojin rundunar Operation Hadin Kai da ke yaki da tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Shugaban a yayin ziyarar ya yi jawabi ga sojojin sojojin Najeriya a hedikwatar rundunar Operation Hadin Kai da runduna ta 7 ta sojojin Najeriya da Maiduguri Malari Cantonment a birnin Maiduguri.

Ga wasu mahimman bayanai guda 11 da shugaban ya yi a cewar wata sanarwa da Legit.ng ta samu.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Dan Majalisa Ya Tabbar da Sace Daliban Yauri Na Jihar Kebbi

Muhimman Abubuwa 11 da Shugaba Buhari Ya Bayyana a Ziyararsa ta Jihar Borno
Shugaba Buhari na Najeriya yayin ziyara a jihar Borno | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ga muhimman abubuwa 11 da shugaban ya fada a cewar wata sanarwa da aka samu ga Legit.ng.

1. Aika ta'aziya ga iyalan wadanda suka mutu

Kamar yadda na aika da sakon ta'aziyata ga iyalan jarumanmu da suka mutu, ina addu’a ga rayukan wadanda suka mutu. Bugu da kari, za mu ci gaba da tabbatar da cewa 'yan uwanmu da suka ji rauni sun sami kyakkyawar kulawa ta likita don murmurewa da samun cikakkiyar lafiyar.

2. Kun sanya ana morar zaman lafiya a arewa maso gabas

Kokarin ku na gama kai ne ya haifar da zaman lafiya da ake mora yankin a yau. A karkashin kulawa ta, an tanadar wa Sojojin Najeriya da dabaru da kuma cikakkiyar ma'ana da alkibla don kiyaye 'yanci da cikakken yankin kasar.

3. Kada a ba wa abokan gaba sararin numfashi

Bai kamata mu ba abokan adawarmu dama ko sararin numfashi ba saboda su kalubalanci ko bata bukatunmu na kasa da mahimman halayenmu.

4. FG ta kagu wajen cin nasarar yaki da ta'addanci

Ya kamata jami'an tsaro su tabbatar da kudurin gwamnatin tarayya na cin nasara a yaki da ta'addanci da barna.

5. Ina mai farin ciki da hadin kan dake tsakanin sojoji

Ina mai matukar farin ciki da lura da karuwar fahimta da hadin kai a tsakanin sojoji, gami da hadin gwiwar cibiyoyin yaki da ‘yan ta’adda da sauran masu laifi a arewa maso gabas.

6. Zuba jari a ayyukan sojoji zai ci gaba

Tare da saka hannun jari a kokarin ci gaba da sake ginawa, za mu ci gaba da saka hannun jari a kan sojoji ta hanyar da za ta daidaita tsarin yaki da ta'addanci.

7. Kayan aiki na gab da fara shigowa Najeriya

Da yawa an shigo dasu sansanin nan, kuma nan ba da dadewa ba za a tura sauran kayan aikin da suka shigo kasar zuwa sansanin nan. Za a sayi karin kayan aiki sosai ga sojojin don biyan bukatu na gajeren lokaci da na dogon lokaci.

8. Yabon shugabannin Sojoji

Ina so, a wannan lokacin in kuma yaba wa shugabannin rundunar sojojinmu saboda hangen nesa da suke yi na tabbatar da cewa an kirkiri wasu kayan aikin soji a cikin gida.

Gyara da inganta wasu daga cikin wadannan mahimman makamai a yanzu ana aiwatar da su a cikin kasar nan ta yadda za a ceto kasar daga kashe kudadenta ga kasashen waje da dama da kuma samar da ayyukan yi ga yawan jama'ar da muke dashi.

9. Ayyukan Gwamnati na ci gaba

Wannan gwamnatin za ta ci gaba da aiki don samar da kudade a kan kari da kuma sayo kayan aiki ga sojoji da sauran hukumomin tsaro. Wannan zai yiwu ne don a habaka yakin dake gudana domin ya zama mai ma'ana ta hankali kuma don biyan bukatunmu da jin dadinmu.

10. Jin dadin ku yana da mahimmanci a gare mu

Jin dadinku da damuwarku na da matukar muhimmanci ga wannan gwamnatin. Na yi murna da juyawar dakaru a hankali a filin daga, kamar yadda na umarta na ya fara. Na tabbata cewa wannan zai rage da kuma zai kawar da gajiyawar yaki, tare da habaka kwarin gwiwar sojoji.

11. Na gode

Ina so in gode muku saboda biyayya da sadaukar da kai da kuka yi don kare kasarmu. karfin zuciyar ku da jaruntarku za su ci gaba da ba wasu kwarin gwiwa.

KU KARANTA: Badakala: Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Wani Babba a Jami'iyyar APC

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya umarci sojoji da su kara himma a yaki da rashin tsaro "saboda akwai aiki da yawa da za a yi." Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga sojojin rundunar hadin gwiwa a filin Maimalari Cantonment a cikin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Buhari ya isa filin faretin Maimalari daidai karfe 11:30 na safe kuma ya samu tarba daga gamayyar sojoji da ‘yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel