Da Ɗuminsa: Boko Haram ta naɗa sabon shugaba bayan tabbatar da mutuwar Sheƙau

Da Ɗuminsa: Boko Haram ta naɗa sabon shugaba bayan tabbatar da mutuwar Sheƙau

  • Kungiyar 'Jama’atu Ahlus Sunna Lidda’awati Wal Jihad' da aka fi sani da Boko Haram ta yi sabon shugaba
  • Sabon shugaban shine Bakura Modu wanda ya yi jawabi a bidiyon da kungiyar ta fitar a baya-bayan nan kamar yadda wata majiya ta tabbatar
  • A cikin bidiyon, Bakura Modu ya karfafawa mayakan kungiyar gwiwa tare da jadada cewa za su dauki fansar kisar Shekau

Kungiyar Boko Haram ta tabbatar da mutuwar shugabanta Abubakar Shekau a cikin wani hoton bidiyo da ta fitar sannan ta nuna sabon shugabanta, Bakura Modu, wanda ya lashi takobin daukar fansar kisan da aka yi tsohon shugabansu Shekau.

VOA ta ruwaito cewa wata majiya da ke kusanci da kungiyar Boko Haram ne ta samarwa kamfanin dillancin labarai na AFP bidiyon, sannan wata majiyar daban ta tabbatar wanda ke jawabin wato Bakura Modu shine sabon shugaban kungiyar.

Mayakan Kungiyar Boko Haram
Mayakan Kungiyar Boko Haram yayin wani hari da suka kai a kauyen Borno. Hoto: The Citizen
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Dakatar da Twitter ya hana wa gwamnonin PDP kafar yaɗa labaran ƙarya, Fadar Shugaban ƙasa

Bidiyon ya haska Bakura tare da wasu mayakan kungiyar a zagaye da shi a bayansa tamkar dai yadda kungiyar ta saba yi a duk lokutan da za ta fitar sa sanarwar makamancin wannan kamar yadda VOA ta ruwaito.

Bakura ya karfafawa yan kungiyar ta 'Jama’atu Ahlus Sunna Lidda’awati Wal Jihad' gwiwa yana mai cewa kada su karaya wurin yaki da abokan gaba duba da abin da ya samu Shekau.

Kazalika, ya yi kira a gare su da su yi watsi da shugaban ISWAP, Abu Musa Al-Barnawi, yana mai jadada cewa za su cigaba da yaki da ISWAP har sai sun dauki fansar kisar Shekau da wasu kwamandojinsu da aka kashe.

Baraka tsakanin Boko Haram da ISWAP

Kungiyoyin biyu sun raba jiha ne tun a shekarar 2016, a lokacin da ISWAP ta fara kalubalantar matakin Shekau na kaiwa farar hura musulmi da basu ji ba ba su gani ba hari da kuma amfani da mata da yara wurin harin kunar bakin wake.

KU KARANTA: Ana bada tukwicin tabar wiwi ga mutane don su yarda a musu allurar rigakafin korona a Amurka

A wasu rahotannin sun alakanta baraka tsakanin kungiyoyin biyu da rashin gamsuwa kan tsain da Shekau ya bi wajen kashe wasu makuden kudade da ISIS ta bawa Boko Haram a matsayin tallafi, inda aka zargi Shekau da zalunci.

Sama da mutum 40,000 ne suka riga mu gaskiya, yayin da wasu miliyan 2 suka gudu daga muhallansu saboda hare-haren Boko Haram tun da kungiyar ta soma ayyukanta a yankin na Arewa maso Gabas a 2009.

Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga

A wani labarin daban, malaman addinin musulunci da mazauna garin Zaria, a ranar Laraba, sun yi addu'a ta musamman domin neman Allah ya kawo musu dauki game da kallubalen tsaro da ke adabar masarautar da jihar, New Nigerian ta ruwaito.

Daruruwan mutane sun hallarci addu'ar da aka yi ta musamman a filin sallar Idi na Kofar-Gayan Low Cost a Zaria. Al'ummar musulmi yayin da suke sallah.

Daya daga cikin wadanda suka jagoranci taron addu'ar, Tanimu Abubakar, ya ce addu'ar da suka kira ya yi dai-dai da koyarwar Manzon Allah (SAW) da ya koyar da musulmi su rika yin addu'o'i idan fitina ta same su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel