Dalilin da yasa ba zan taba ziyartar Shugaba Buhari a Aso Rock ba, Gwamnan Najeriya
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gazawa a aikinta ga ‘yan Najeriya
- Dan siyasar ya bayyana dalilin da ya sa ba daidai ba ne a dora wa gwamnonin jihohi alhakin tsaro a jihohinsu
- Gwamnan na Ribas ya kuma soki gwamnatin tarayya kan karbar bashi daga kasashen waje
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce ba zai taba kai ziyara fadar shugaban kasa don neman taimakon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan wata matsala ba.
Wike ya yi wannan bayanin ne a ranar Talata, 15 ga watan Yuni, lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da wani aikin hanya a karamar hukumar Etche (LGA) ta jihar Ribas.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, na shirin kayyade karin kayayyakin kasashen waje a dokar shigo da kaya
Ya zargi shugaban kasar da daura nauyin da ya rataya a wuyan shi na tsaron ‘yan Najeriya ga gwamnoni, kamar yadda PM News ta ruwaito.
Wike yayi ikirarin cewa gwamnatin Buhari bata da dabaru
A cikin wata sanarwa da Kelvin Ebiri, mai magana da yawunsa ya fitar, an kuma ambato gwamnan yana cewa gwamnatin Buhari ba ta da dabarun dawo da zaman lafiya a duk fadin kasar.
Wike ya ce wasu gwamnoni a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) suna da dabi'ar rugawa fadar shugaban kasa lokacin da ya kamata su zauna a jihohin su kuma su biya bukatun mutanen da suke mulka.
Ya ce:
“Ya kamata Shugaban kasa ya fito fili ya ce, gwamnonina na APC, ku daina damu na. Ku koma jihohin ku kuyi aikin ku. A kan haka, ina goyon bayansa.
“Godiya ga Allah, Shugaban kasa ya san cewa ba na daga cikin wadanda za su ziyarce shi kan wata matsala ko wani abu. Ni, a matsayina na gwamnan Ribas karkashin PDP, ba za ka taba samuna a wurin ba.”
Gwamnan yace Buhari shine babban kwamanda
A cewar jaridar The Cable, Wike ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta yarda cewa ba za ta iya sake cika alkawurran da ta daukar wa ‘yan Najeriya ba, sannan ta yi kokarin jagorantar kasar nan daga matsalolin da take fuskanta.
Ya ce Buhari shi ne babban kwamandan rundunar soja kuma shi kadai ke da alhakin tsare kasar.
Hirarmu da Buhari ta tabbatar da shi ne ke tafiyar da gwamnatinsa, yana sane da komai: Reuben Abati
A wani labarin, Reuben Abati, wanda tsohon kakakin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ne, ya ce ta tabbata cewa Shugaba Muhammadu Buhari shi ne ke tafiyar da akalar kasar nan.
Yana magana ne kan hirar da Shugaban ya yi da gidan telebijin din ARISE a makon jiya.
Masu suka da dama ciki har da Wole Soyinka da Aminu Tambuwal Gwamnan Jihar Sakkwato sun yi ikirarin cewa wadansu mutane ne na daban ke jan akalar harkokin kasar nan suna masu cewar Shugaba Buhari ba ya tafiyar da mulkin kasar.
Asali: Legit.ng