Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, na shirin kayyade karin kayayyakin kasashen waje a dokar shigo da kaya

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, na shirin kayyade karin kayayyakin kasashen waje a dokar shigo da kaya

  • Za a takaita ko cire wasu kaya daga dokar shigo da kaya, saboda gwamnati na son rage adadin yadda ‘yan Najeriya da ke cin kayayyakin kasashen waje
  • Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na shirin rage dokar shigo da kayayyaki da kashi 35%
  • Shugaban manufofin hadahadar kudi na Najeriya ya ce kasar na tafiya yadda ya kamata saboda rage shigo da kaya da ta yi a baya, kuma idan aka kara yin ragin, kasar za ta inganta

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, na shirin toshe karin abincin kasashen waje da ake shigowa da su kasar duk da hauhawar farashin kayayyaki.

Emefiele ya ce gwamnati na shirin yanke shigo da kayayyakin da kashi 35%, yayinda shirin cire wasu abinci ko kayayyaki daga dokar shigo da kayayyaki ya fara ba da sakamako mai kyau.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Ma'aikatan Lafiya Sun Fara Yajin Aiki, Sun Bada Mahimman Dalilai

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, na shirin kayyade karin kayayyakin kasashen waje a dokar shigo da kaya
Gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele Hoto: next24online/Nur
Asali: Getty Images

Idan aka taƙaita ƙarin kayayyaki, za a toshe su daga jerin abubuwan da suka cancanci amfani da su a hada-hadar chanjin kudade na kasashen ketare, wanda ake buƙata don shigo da kayayyaki. Wannan zai haifar da hauhawar farashin kaya idan aka samu dala a kasuwannin bayan fage.

Takaitawar da rufe kan iyaka sune musabbabin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, wanda a yanzu yake da kashi 17.93% a watan Mayu, kodayake ya sauka daga 18.12% watan Afrilun 2021.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta zargi gwamnonin PDP da kin kawo karshen rikicin makiyay

Najeriya a yanzu tana cin gajiyar toshe kayayyakin kasashen waje

Ya ce rage yawan cin abincin kasashen waje ya taimaka wa kasar wajen samun rara a kan chanjin kudaden kasashen waje da bunkasa harkokin cikin gida, musamman bangaren noma.

Gwamnan ya yi amfani da matatar Dangote a matsayin daya daga cikin masana'antar cikin gida da za ta taimaka wajen rage dokar shigo da kayayyaki. A cewar shugaban bankin na kasa, ba da dadewa ba kasar za ta hana shigo da kayayyakin man fetur da zarar matatar ta fara aikinta.

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ban girma daga Buah Saidy, Gwamnan Babban Bankin na Gambiya. Emefiele ya ce dagewar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi game da bunkasar tattalin arziki shekaru biyar da suka gabata a yanzu tana amfanar kasar a hankali.

A wani labarin, Kamfanin MTN ya yi gargadin yiwuwar dakatar da ayyukansa a Najeriya sakamakon karuwar matsalar rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar, TheCable ta ruwaito.

MTN, a wani sako da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya gani, ya sanar da kwastomominsa game da yiwuwar jinkiri a hulda dashi.

“Abin takaici, dole ne mu sanar da ku cewa tare da karuwar rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya; zaku iya samun tseko a sabis dinmu a cikin kwanaki masu zuwa,” kamar yadda aka ruwaito MTN ya ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel