Ana bada tukwicin tabar wiwi ga mutane don su yarda a musu allurar rigakafin korona a Amurka
- Jihar Washington a Amurka ta fara bawa mutane ganyen tabar wiwi kyauta idan an musu rigakafin korona
- An bullo da wannan shirin bada tukwuicin ne a matsayin karfafa gwiwa ga mutane su tafi su yi rigakafin
- Wasu jihohin Amurka kamar Arizona itama ta bullo da wani shirin makamancin wannan ba bawa mutane tabar wiwi don su yi rigakafi
A wani yunkuri na karfafawa mutane gwiwa su tafi a yi musu allurar riga kafin Covid-19, wasu wuraren sayar da tabar wiwi a jihar Washington, Amurka sun fara bawa mutane kyautan wiwi bayan an musu riga kafin, The Cable ta ruwaito.
Mahukunta a hukumar bada lasisin giya da wiwi, LCB, sun ce, "masu sana'ar sayar da wiwi da dama sun tuntube su domin a basu daman su rika bawa mutane kyauta domin a karfafa musu gwiwa su yi rigakafin."
DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC ya sake galaba kan ɗan takarar PDP a kotun ɗaukaka ƙara a Ondo
Hukumar ta LCB, a ranar 7 ga watan Yuni ta bawa masu sayar da wiwi damar su rika bada kyautar 'wiwi' ga masu sha inda an musu rigakafin korona a cibiyoyin yin rigakafin, Nigerian Eye ta ruwaito.
A cewar hukumar ta LCB, an bullo da tsarin ne mai suna 'Joint for Jabs' domin karafafawa mutanen jihar su tafi suyi karbi rigakafin.
An yi wannan garabasar ne daga ranar 7 zuwa 12 ga watan Yuni, sannan mutanen da shekarunsu ya haura 20 ne kawai za su iya amfana da garabasar a ranar da aka yi musu rigakafin.
A makon da ta gabata hukumar ta LCB ta bada lasisi da wasu kamfanonin da suka rika bawa mutane kyautan giya da wasu ababen sha idan an musu rigakafin.
KU KARANTA: An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe
Washington ba itace kadai jihar Amurka da ke bawa mutane tabar wiwi idan an musu rigakafin korona ba.
Wani shagon siyar da magunguna a Arizona a shirinsa na 'Snax for Vaxx' shima ya bawa mutanen da suka yi rigakafin kyautar ganyen na tabar wiwi matukar shekarunsu ya kai 21.
Tun bullar annobar, mutane kimanin miliyan 33 ne suka kamu da ita a Amurka inda kimanin 600,000 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.
A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.
Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.
Asali: Legit.ng