Hirarmu da Buhari ta tabbatar da shi ne ke tafiyar da gwamnatinsa, yana sane da komai: Reuben Abati

Hirarmu da Buhari ta tabbatar da shi ne ke tafiyar da gwamnatinsa, yana sane da komai: Reuben Abati

  • Shugaba Buhari ya yi hira da kafar telebijin sannan ya sake yi wa al’ummar Najeriya jawabi
  • Wanda yayi hira da shi ya karyata jita-jitar cewa Buharin ba shi ke jan akalar gwamnatinsa ba
  • Hirar ta kara fito da bambancin da ke tsakanin ’yan Najeriya

Reuben Abati, wanda tsohon kakakin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ne, ya ce ta tabbata cewa Shugaba Muhammadu Buhari shi ne ke tafiyar da akalar kasar nan.

Yana magana ne kan hirar da Shugaban ya yi da gidan telebijin din ARISE a makon jiya.

Masu suka da dama ciki har da Wole Soyinka da Aminu Tambuwal Gwamnan Jihar Sakkwato sun yi ikirarin cewa wadansu mutane ne na daban ke jan akalar harkokin kasar nan suna masu cewar Shugaba Buhari ba ya tafiyar da mulkin kasar.

Yayin da wadansu kuma suke da’awar cewa masu magana da yawun Shugaban sune ke fadar ra’ayoyinsu na kashin kai maimakon na maigidan nasu.

Reuben Abati ya magantu
Hirarmu da Buhari ta tabbatar da shi ne ke tafiyar da gwamnatinsa, yana sane da komai: Reuben Abati Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Twitter

Amma Reuben Abati, wanda yana daga cikin ayarin ’yan jaridar da suka yi hirar da Shugaban Kasar ya ce hirar ta tabbatar da cewa Shugaba Buharin yana sane da dukkanin abubuwan da ke tafiya a kasar.

Ya ce Shugaban shi ne ke tafiyar da gwamnatinsa sannan bai nuna alamun kwan gaba kwan baya ko kuma i’ina kan matsayarsa da aka san shi da su a baya duk kuwa da cewa ra’ayoyin nasa suna cike da ce-ceku-ce.

“Hirar tamu da shi ta tabbatar da cewa ko shakka babu Shugaba Muhammadu Buhari shi ne ke iko da gwamnatinsa. Yana da cikakkiyar masaniyar ababuwan da ke faruwa a kasar nan. Sannan bai nuna alamun inda-inda ko kame-kame a fadar ra’ayoyinsa da aka san shi da su duk da cewa suna cike da ce-ce-ku-ce.,’’ Inji Abati.

Abatin ya ci gaba da cewa hirar ta kara fito fili da bambance-bambancen da ke tsakanin al’ummomin kasar nan a matsayinta na kasa daya.

Buhari ya rika yiwa yan Najeriya magana akai-kai

Sannan ya bukaci Shugaban da ya doge wajen yi wa ’yan Najeriya jawabi lokaci zuwa lokaci.

“Duk wanda ya shawarci Shugaban da ya yi hirar a ranar Alhamis sannan ya yi wa al’ummar kasa jawabi ranar Asabar alal hakika ya taimake shi sosai. Tasirin bayyana a kafofin labarai yana da girman gaske, duk da cewa ya zo a makare, amma dai ya fi a ce bai yi ba sam-sam,” inji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel