Da dumi-dumi: Ma'aikatan Lafiya Sun Fara Yajin Aiki, Sun Bada Mahimman Dalilai
- Ma’aikatan lafiya a asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin (UITH) sun fara yajin aikin gargadi
- Olutunde Oluwawumi, shugaban kungiyar ma’aikatan lafiyan, ya ce matakin ya zama mai muhimmanci bayan da shugabannin asibitin suka gaza aiwatar da bukatunsu
- Bukatun sun hada da gyara tsarin da ya lalace, biyan bashin karin girma na shekaru uku na ma’aikata, da sauransu
Mambobin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH) Kungiyar Hadin Kan Lafiya (JOHESU) a ranar Laraba sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa sun shiga yajin aikin ne don zanga-zanga kan rashin kyawun aiki, lalacewar gine-gine da kayan aiki marasa amfani a asibiti.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: APC ta dakatar da Sharada, dan majalisa mai adawa da Ganduje
Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kungiyar JOHESU a asibitin, Olutunde Oluwawumi ya umarci dukkan mambobin da su bar ofisoshinsu su daina aiki ba tare da bata lokaci ba har sai shugabannin sun amsa musu bukatunsu.
Daga cikin sauran batutuwan, Kwamared Oluwawumi ya ce shugabannin asibitin sun ki biyan bashin karin girma na shekaru uku na ma’aikata a cikin shekaru ukun da suka gabata.
KU KARANTA KUMA: 2023: Ibrahim Shekarau ya bayyana daga yankin da ya kamata APC ta fitar da dan takarar Shugaban kasa
Ya kara da cewa har yanzu hukumar ba ta kammala shirin karin girma na ma'aikata ba a shekarar 2021.
Da yake maida martani, kakakin asibitin, Olabisi Ajiboye, ya ce hukumar na duba koken ma’aikatan.
NLC Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani Saboda Mafi Ƙarancin Albashi
A wani labari makamanin haka, kungiyar kwadugo, NLC, ta sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani a jihar Nasarawa saboda jan ƙafa da gwamnati ke yi wajen aiwatar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata da kuma walwalarsu.
The nation ta ruwaito cewa, NLC ta umarcin dukkan ƙungiyoyin ma'aikatan jihar da su tsunduma yajin aiki wanda aka shirya zai fara daga tsakiyar daren Talata, 15 ga watan Yuni.
An bayyana shiga yajin aikin a ranar Litinin 14 ga watan Yuni, a babban birnin jihar, Lafiya, bayan fitowa daga taron da ɓangaren zartarwa suka gudanar tare da ƙungiyoyin ƙwadugo.
Asali: Legit.ng