Dalla-Dalla: Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarabawar JAMB 'Mock' 2021

Dalla-Dalla: Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarabawar JAMB 'Mock' 2021

  • Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar gwaji da ta gudanar
  • Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar JAMB, Dr Fabian Benjamin, ya fitar
  • Yace dalibai 62,780 suka zauna jarabawar kuma zasu iya ganin sakamakon su a shafin JAMB na yanar Gizo

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta saki sakamakon jarabawar gwaji da aka gudanar ranar 3 ga watan Yuni, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Kasar Saudiyya Ta Yanke Wa Wani Matashi Hukuncin Kisa Kan Laifin da Ya Aikata Tun Yana Yaro

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani gajeren jawabi da kakakin JAMB, Dr Fabian Benjamin, ya fitar ranar Laraba.

Yace: "Mun saka Sakamakon jarabawar gwaji da aka gudanar ranar 3 ga watan Yuni a shafin mu na yanar gizo-gizo. Duk ɗalibin da ya zauna jarabawar zai iya duba sakamakon shi a shafin."

JAMB ta fiyar da sakamakon jarabawar gwaji 2021
Da Ɗumi-Ɗumi: Hukumar JAMB Ta Saki Sakamakon Jarabawa 2021 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa mutum 160,718 ne suka nuna sha'awar zana jarabawar gwajin, amma 62,780 ne kacal suka samu ikon zama jarabawar, kamar yadda punch ta ruwaito.

Za'a fara gudanar da asalin jarabawar share fagen shiga manyan makarantun gaba da sakandire ne daga ranar 19 ga watan Yuni.

KARANTA ANAN: Cikakke Bayani: INEC Ta Bayyana Sabon Adadin Runfunan Zaɓe a Najeriya, Ta Soke Wasu 746

Yadda zaka duba sakamakom jarabawar gwaji ta JAMB

1. Da farko zaka ziyarcin shafin yanar gizo na hukumar JAMB https://jamb.gov.ng/efacility

2. Daga nan saika shiga wurin da aka ware na sakamakon gwaji 2021.

3. Zaka ga wani wuri an ce ka saka lambar jarabawarka ta JAMB. Bayan ka sanya lambar saika danna wurin 'Duba Jarabawar gwaji 2021'

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Ƙi Sakin Wani Basarake, Sun Saki Matansa Biyu Duk da An Basu Maƙudan Kuɗi

Yan bindiga sun saki matan Madakin Zungeru, ƙaramar hukumar Wushishi, jihar Neja, bayan an biya kuɗin fansa miliyan N5m.

Yan bindigan sun cigaba da riƙe madakin Zungeru saboda ba a basu cikakken kuɗin da suka bukata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel