Da duminsa: EFCC ta gurfanar da jami'an gwamnatin Sokoto 5 kan damfarar N500m
- Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu jami'an gwamnatin jihar Sokoto 5 a gaban kotu
- An kama su da laifin cin amana tare da sace kudin sallamar malaman makaranta har N500m
- Sun cire kudaden fansho da na sallamar malaman firamaren daga asusun bankin da aka adana
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da ma'aikatan hukumar fansho ta makarantar firamare a kan zarginsu da ake da waskar da kudi har N553.985,644.1.
Kudin an adana shi ne domin biyan malaman makaranta da suka yi ritaya kudin sallama da na fansho, Daily Trust ta ruwaito.
Ma'aikatan sun hada da: Abubakar Aliyu, Hassana Moyi, Haliru Ahmad, Kabiru Ahmad da Dahiru Muhammad Isa.
KU KARANTA: Faruk Yahaya: Ina da gogewa a fannin yaki, zan iya shawo kan matsalar tsaron Najeriya
KU KARANTA: Ahmed Musa yayi martani mai zafi bayan sun sha da kyar a filin wasa a Kaduna
An gurfanar da ma'aikatan gaban babbar kotu
An gurfanar da jami'an a gaban wata babbar kotu a Sokoto a kan laifuka 28 da suka hada da cin amana da almundahana wanda suka ci karo da sashi na 92, sakin layi na biyu na dokokin Penal Code.
A yayin bayani, shugaban EFCC na yankin, Usman Bawa Kaltungo, ya ce ma'aikatan sun yi amfani da sa hannun bogi inda suka cire kudin sallamar malamai da na fansho a jihar.
Yadda aka cire kudin
Kaltungo wanda yace yayi aiki ne kan korafin da daya daga cikin masu fanshon ya kawo masu, ya ce tsakanin 17 na watan Janairun 2017 zuwa watan Maris na 2020, daraktan kudin ya cire kudi da ya kai miliyan 83.2 daga asusunsu na banki.
"A wannan lokacin, Halliru da Kabiru sun cire 203,217,770.71 da 266,567,053 daga asusun bankin da sunan 'yan fanshon," yace kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
“Da kanmu muka biya kudin motan wasu daga cikin 'yan fanshon domin su zo bada shaida, sun matukar girgiza ganin cewa kudaden da suka dade suna tarawa aka waskar."
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci garin Maiduguri dake jihar Borno a ranar Alhamis na kwana daya, inji Gwamna Babagana Umara Zulum.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Talata a gidan gwamnatin jihar dake Maiduguri inda yace shugaban kasan zai duba yanayin halin da tsaron yankin arewa maso gabas yake ciki, Channels TV ta ruwaito.
A yayin ziyarar, ya ce shugaban kasan zai kaddamar da gidaje 4,000 wadanda suke daga cikin aikin gidaje na gwamnatin tarayya tare da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar.
Asali: Legit.ng