Yan Bindiga Sun Ƙi Sakin Wani Basarake, Sun Saki Matansa Biyu Duk da An Basu Maƙudan Kuɗi

Yan Bindiga Sun Ƙi Sakin Wani Basarake, Sun Saki Matansa Biyu Duk da An Basu Maƙudan Kuɗi

  • Yan bindiga sun cigaba da riƙe madakin Zungeru saboda ba a basu cikakken kuɗin da suka bukata
  • Sai-dai sun saki matansa biyu, waɗanda suka sace tare da Basaraken, Mustapha Madaki
  • Yan bindingan sun buƙaci a basu miliyan N10m da wayoyi 100, amma sai aka kai musu miliyan N5m

Yan bindiga sun saki matan Madakin Zungeru, ƙaramar hukumar Wushishi, jihar Neja, bayan an biya kuɗin fansa miliyan N5m, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane

A kwanakin baya ne, yan bindiga suka kutsa har cikin gidan basaraken, Mustapha Madaki, suka yi awon gaba da shi da kuma matan shi guda biyu.

An biya maƙudan ƙuɗi a matsayin fansa amma sun ƙi sakin Basaraken

Wata majiya daga ƙaramar hukumar ta bayyana cewa bayan ɗaukan wasu kwanaki ana tattaunawa da yan bindigan. Mutanen garin sun haɗa miliyan N5m daga cikin miliyan N10m da yan bindigan suka nemi a basu da farko.

Yan bindiga sun cigaba da riƙe basaraken Neja
Yan Bindiga Sun Ƙi Sakin Wani Basarake, Sun Saki Matansa Biyu Duk da An Basu Maƙudan Kuɗi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Bayan tsabar kuɗi miliyan N10m, yan bindigan sun buƙaci a basu manyan wayoyin android guda 100, da mashin Bajaj guda 5, kuma akai su wani wuri da suka faɗa a yankin Madaka, karamar hukumar Rafi.

Majiyar tace: "Da farko yan bindigan sun buƙaci a basu kuɗi naira miliyan N10m, wayoyin hannu 100 da kuma mashin bajaj guda 5, amma a halin yanzun bamu haɗa waɗannan kuɗi ba."

KARANTA ANAN: Abun Tausayi: Iyayen Ɗaliban Islamiyya da Aka Sace a Neja Sun Fara Bin Masallatai, Coci Suna Roƙon Kuɗi

Legit.ng hausa ta gano cewa masu garkuwan sun buƙaci a ƙara musu kuɗi kafin su saki basaraken.

Wani rahoto ya bayyana cewa an kai mata 2 da aka sako wani asibiti a Abuja domin kula da lafiyarsu.

A wani labarin kuma Babban Dalilin da Yasa Ba Zamu Taɓa Rabuwa da Almajiranci a Arewa Ba, Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano , yace gwamnonin arewa ba dagaske suke ba wajen ɗaukar mataki a kan kwararar almajirai a jihohinsu, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan yace ya zama wajibi gwamnonin jihohi su haɗa kan su sun ɗauki matakin daƙile matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel