Mai Jiran Gadon Sarauta Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Wajen Tantance Shi

Mai Jiran Gadon Sarauta Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Wajen Tantance Shi

  • Wani mai neman sarauta ya yanke jiki ya fadi a wajen zaben sabon sarki a wani yankin jihar Ondo
  • An ruwaito cewa, mutumin yana daga cikin mutanen da ke takarar kujerar saurauta da ake zaben akanta
  • An ce ya yanki jiki ya fadi ba zato ba tsammani, inda ya mutu nan take, lamarin da ya tsorata jama'a

Wani daga cikin masu neman sarautar Akunu-Akoko a karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma a jihar Ondo, Olorundare Agooye a ranar Lahadi ba zato ba tsammani ya mutu a wurin zaben wanda za a nada, Sun News ta ruwaito.

An tattaro cewa masu neman sarautar sun hadu ne a Oke Ima, wurin da za a gudanar da zaben tare da manyan sarakunan yankin da ake kira 'Warrant Chief' da gwamnatin jihar ta amince dasu domin tantance sarakunan, kwatsam sai Agooye ya yanki jiki ya fadi matacce.

KU KARANTA: Da Duminsa: 'Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Kaca-Kaca da Sansanin Sojoji a Borno

Mai Jiran Gadon Sarauta Ya Mutu a Wajen Zaben Sabon Sarki a Jihar Ondo
Taswirar jihar Ondo a kudu maso yammacin Najeriya | Hoto: researchgate.net
Asali: UGC

Marigayin, kamar yadda aka samu labari, zai yi takara da wani mutum kafin mutuwa ta mishi sallama ba zato ba tsammani.

Jami'an karamar hukumar ta Akoko North Ewst ne suka kula da aikin zaben.

Nadin ya zama dole saboda yawancin masu sarauta a garin babu su kuma ana cike da matukar bukatar nadin kujerar, kamar yadda The Nation ta shaida a rahoton ta.

Gwamnatin jihar tana bukatar nada shuwagabannin da take kira da 'Warrant Chiefs' don maye gurbin hakiman masarautu wadanda suka shude domin zabar sabon sarki ga Akunu Akoko.

KU KARANTA: Kamfanin MTN Zai Tattara Komai Nashi Ya Fice Daga Najeriya Saboda Wasu Dalilai

A wani labarin, Daily Trust ta ruwaito Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, a ranar Litinin yana cewa garin Zaria na cikin mamayar 'yan ta'adda.

A cewarsa, mazauna garin ba sa iya bacci saboda sace-sacen mutane da ke gudana a tsakanin garin Zariya da kewaye.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, Sarkin ya bayyana lamarin a matsayin abinda ba za a yarda da shi ba don haka ya bukaci gwamnati ta dauki mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel