Da Duminsa: 'Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Kaca-Kaca da Sansanin Sojoji a Borno

Da Duminsa: 'Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Kaca-Kaca da Sansanin Sojoji a Borno

  • Rahotanni daga jihar Borno sun bayyana cewa, wasu maharan ISWAP sun kai hari sansanin sojoji
  • Rahoton ya bayyana yadda lamarin ya faru, yayin da 'yan ta'addan suka yi awon gaba da motocin soji
  • Hakazalika sun yi kaca-kaca da sansanin, in da suka bankawa wajen wuta suka tsere da makamai

Wasu masu tayar da kayar baya da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne sun mamaye wani sansanin sojoji a kudancin jihar Borno a ranar Talata sannan suka kwashe makamai bayan wani kazamin artabu da sojojin, in ji rahoton Daily Trust.

An gano cewa mayakan sun zo cikin motoci kusan 10 domin yin kawanya ga rundunar da aka kafa a kauyen Kwamdi, da ke karamar hukumar Damboa da yammacin ranar Talata.

An ce sun kone manyan makaman soji na 'Ammour Persnal Carrier (APC)' da motar bindiga.

A cewar wani memba na kungiyar jami'an hadin gwiwa ta JTF, Hamidu Abu, kungiyar ta'addancin ta faki sansanin sojoji ne amma ba mazauna yankin ba.

KU KARANTA: Kamfanin MTN Zai Tattara Komai Nashi Ya Fice Daga Najeriya Saboda Wasu Dalilai

Da Duminsa: 'Yan Ta'addan ISWAP Sun Bankawa Sansanin Sojoji Wuta a Jihar Borno
Labari da dumi-dumi daga jaridar Legit.ng Hausa | Hoto: legit.ng
Asali: Original

Ya kuma bayyana cewa an lalata sansanin kamar yadda maharan suka sace makamai da alburusai suka tsere.

Yake cewa:

“Sun zo da misalin karfe 4 na yamma kuma saboda guguwar yashi ya zamana mai matukar wuya sojoji su fatattake su. Sun kona sansanin har da APC da wasu motoci hudu.
"Ba zan iya tabbatar da cewa ko akwai wani jin rauni da aka gano ba."

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan ta'addan ISWAP ne sun kaiwa sansanin hari da misalin karfe 4 na yamma kuma ya dauki kimanin awa daya da mintuna 30.

Majiyar ta kara da cewa mayakan sun yi amfani da damar guguwar yashi wajen kutsa kai cikin sansanin.

Majiyar tsaron ta fada cewa:

"An kawo mana hari a sansaninmu da ke Kwamdi amma ba mu rasa ko daya daga cikin dakarunmu ba, amma abin takaici sansanin ya yi kaca-kaca."

Babu wani martani a hukumance daga sojojin na Najeriya har zuwa yanzu.

KU KARANTA: Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ke Noman Doya a Cikin Buhunna Ba a Gona Ba

Da Duminsa: Boko Haram ta sako Alooma da wasu mutum 9 da ta sace watanni 5 da suka gabata

A wani labarin, Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta sako babban mataimaki na kariya a Hukumar Kula da' Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Alooma da ta sace a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, The Nation ta ruwaito.

Majiyoyi daga hukumomin tallafawa al'umma sun tabbatar da cewa Alooma yana asibitin dakarun sojoji na Operation Hadin Kai a Maiduguri ana duba shi kafin a sada shi da iyalansa.

Majiyar ta kuma ce an sako dan kasuwa, Mu'azu Bawa, wanda aka sace shi tare da wasu mutane takwas a ranar, duk dai sojoji na musu tambayoyi da duba su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: