Shugaban hukumar NDLEA a Ondo Haruna Gagara ya riga mu gidan gaskiya

Shugaban hukumar NDLEA a Ondo Haruna Gagara ya riga mu gidan gaskiya

  • Haruna Gagara, shugaban hukumar NDLEA na jihar Ondo ya riga mu gidan gaskiya
  • Gagara, ya mutu yana da shekaru 59 a duniya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Hukumar NDLEA reshen jihar Osun ta tabbatar da rasuwarsa tana mai cewa an yi rashin jajirtaccen shugaba

Babban Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, na jihar Ondo, Mr Haruna Gagara ya rasu yana da shekaru 59 a duniya, Daily Trust ta ruwaito.

Hukumar ta NDLEA reshen jihar Ondo ta tabbatar da rasuwarsa tana mai cewa mutuwarsa ya girgiza su.

Shugaban NDLEA na Jihar Ondo, Haruna Gagara
Babban Kwamandan NDLEA na Jihar Ondo, Haruna Gagara. Hoto: TVC News
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zanga-Zanga ta ɓarke gidan yari yayin da gandireba ya bindige wani baƙo har lahira

Tvc News ta ruwaito cewa ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Mai magana da yawun hukumar, Mr Ekechuku Wilson ya tabbatar da rasuwar Gagara.

Wilson ya ce tsohon mai gidansa wanda aka haifa a 1962, ya fito ne daga karamar hukumar Lantan na jihar Plateau.

Ya kara da cewa Gagara jami'i ne mai jajircewa da a wurin aiki tare da bin dokoki sau da kafa a lokacin da ya ke jagoranci da kuma ayyukansa da ya yi a sassan kasar.

KU KARANTA: An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe

Marigayin shugaban na NDLEA ya rasu ya bar matan aure da yara.

A cewar mai magana da yawun hukumar na NDLEA, za a yi addu'o'i na musamman a ranar Laraba misalin karfe 3pm a cocin hukumar da ke hedkwatarsu da ke Alagbka Akure a jihar Ondo.

A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel