Babban Hadimin Gwamna Ya Tsallake Rijiya Ta Baya, an Yi Awon Gaba da Shanunsa
- Wasu mahara sun dira gidan babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Benue kan harkokin gidan gawamnati
- Harin na 'yan bindiga bai zo da asarar rai ba, amma an ruwaito mutane da dama cewa sun ji raunuku
- An sanar da rundunar 'yan sandan jihar, kuma ta bayyana cewa tana kan bincike kan lamarin
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Benue kan harkokin kula da gidan gwamnati, Dakta James Anbua, a safiyar jiya ya tsallake yunkurin kashe shi a gidansa dake Tse-Girgi, Mbavuur, karamar hukumar Logo ta Benue, The Guardian ta ruwaito.
Wani ganau, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa maharan da ke kan babura uku sun isa Tse-Girgi ne da misalin karfe 1:30 na rana kuma suka fara harbi a gidansa.
KU KARANTA: Ghali Na’Abba Ya Bayyana Yadda Gwamnoni Suka Jefa Najeriya Cikin Matsaloli
Harin ya zo ne kimanin awanni 10 bayan Anbua ya aurar da 'yarsa, yayin da gidan ke makare da bakin biki.
Ba a rasa rai ba yayin harin, amma mutane da yawa da ke cikin gidan sun ji rauni, kuma maharan sun yi awon gaba da shanu kusan 10 na mai taimakawa gwamnan, Daily Trust ta ruwaito.
An ba da rahoton faruwar lamarin a Ofishin ’yan sanda na Shiyya, Ugba da ke Logo a jihar ta Benue.
KU KARANTA: Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ke Noman Doya a Cikin Buhunna Ba a Gona Ba
A wani labarin, Gwamna Abubakar Bello ya kaddamar da jami'an 'yan banga na musamman na jihar Neja da nufin dakile ayyukan gungun matasa mabarnata, musamman wadanda ke barna a Minna, Punch ya ruwaito.
Bello ya kaddamar da kungiyar 'yan bangan ne na musamman a Hedkwatar 'yan sanda da ke birnin Minna wadanda suka fito daga kungiyoyin tsaro daban-daban na jihar.
A cewar gwamnan, “Yayin da hukumomin tsaro ke fada da 'yan bindiga a yankunan karkara, wani sabon salo ya bullo a Minna wanda ba za a yarda da shi ba.
Asali: Legit.ng