Bamu da lokacin batawa: Shugaba Buhari ya tura sako ga kasashen Afrika

Bamu da lokacin batawa: Shugaba Buhari ya tura sako ga kasashen Afrika

  • Shugaba Buhari ya bayyana bukatar kasashen Afrika ta yamma a kokarin yaki da Boko Haram
  • Shugaban ya bayyana haka ne yayin karbar wani wakilin UNOWAS da aka turo aiki zuwa Najeriya
  • Shugaban ya tabbatar da bada gudunmawa dari bisa dari domin yaki da ta'addanci a yankin Afrika

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ce dole ne kasashen Afirka ta Yamma da ke fama da rikice-rikice su hada karfi da karfe don ceto yankin daga ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP, PM News ta ruwaito.

Shugaban ya yi magana ne a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja, yayin karbar sabon Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na Yammacin Afirka da yankin Sahel (UNOWAS), Mista Mahamat Saleh Annadif, dan kasar Chadi.

Buhari ya ce: “Kai ne makwabcinmu. Kana da kwarewa sosai kan al'amuran da suka shafi yankin Sahel, ka yi shekaru biyar a Mali. Ina fatan za ka sa kasashen su yi aiki tare don tunkarar matsalolin da suka shafe su."

KU KARANTA: EFCC Ta Bayyana Yadda Ake Sace Kudin Najeriya da Bitcoin, Ta Kwato Miliyoyi

Rashin tsaro: Shugaba Buhari ya tura sako ga shugabannin kasashen Afrika
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yayin da yake bayyana matsalolin a matsayin "masu girman gaske," Shugaba Buhari ya lura cewa kungiyar Boko Haram ta hallaka rayukan mutane da albarkatu da dama a cikin Najeriya da wasu kasashe makwabta, yayin da Mali take da yanki mai yawa na kasar da mayakan suka mamaye.

Ya gabatar da cewa: "Ina fata a karkashin kulawar UNOWAS, za ku taimaka a warware matsalolin. Yawancinsu suna da nasaba da rashin zaman lafiya a Libya, kuma abin ya shafe mu duka."

Buhari ya yi alkawarin cewa Najeriya zata bada taimako ga Wakilin na Musamman, don ya samu nasarar aikin da aka ba shi.

Annadif ya ce ya zo ziyarar ne jim kadan bayan nadin nasa, saboda ya fahimci muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa a Afirka ta Yamma.

Ya ce ya san matsalolin yankin Sahel sosai, kuma zai dogara ne da taimakon Najeriya don samun nasara.

KU KARANTA: Shugaban EFCC Ya Bayyana Tsarinsa Na Tabbatar da Ya Karar da Rashawa a Najeriya

Da Dumi-Dumi: Najeriya Za Ta Buga Wa Kasar Gambia Kudade, Ba Sauran Kai Wa Turai

A wani labarin daban, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya amince bisa ka'ida don buga kudin Dalasi na kasar Gambiya, Daily Trust ta ruwaito.

Legit ta tattaro cewa, Gwamnan Babban Bankin, Mista Godwin Emefiele, ya amince da shawarar buga kudin daga Gwamnan Babban Banki na kasar Gambiya, Mista Buah Saidy, wanda ya jagoranci wata tawaga da ta ziyarce shi a ranar Talata.

Mista Emefiele ya ce Najeriya na da karfin gaske a harkar buga kudi kamar yadda take bugawa tun a shekarun 1960 kuma “a shirye muke mu taimaka wajen buga kudinku. Za mu iya kasancewa da araha sosai ta fuskar tsadancewa,” in ji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel