Fulani Makiyaya Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Wasu 6 a Enugu da Akwa Ibom

Fulani Makiyaya Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Wasu 6 a Enugu da Akwa Ibom

  • Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutum ɗaya tare da sace 5 a jihar Enugu
  • Maharan sun nemi iyalan waɗanda abun ya shafa da su biya naira miliyan N10m domin su fanshi yan uwansu
  • A wani harin na daban, wasu makiyaya sun kashe mutum ɗaya a jihar Akwa Ibom

Wasu da ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe mutum ɗaya, tare da sace mutum 6, cikinsu harda mace a yankin Eha-Amufu, ƙaramar hukumar Isi-Uzo, jihar Enugu.

Punch ta ruwaito cewa maharan sun nemi iyalan waɗanda suka sace da su biya miliyan N10m domin su fanshi yan uwansu.

KARANTA ANAN: NLC Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani Saboda Mafi Ƙarancin Albashi

Wata majiya daga yankin da lamarin ya faru, tace maharan sun shiga yankin ne da misalin 7:00 na daren ranar Laraba, 9 ga watan Yuni.

Makiyaya sun kashe mutum biyu, sun sace 6
Fulani Makiyaya Sun Kashe Mutum 2 Tareda Sace Wasu 6 a Enugu da Akwa Ibom Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Rahoton the nation ya bayyana sunan wanda aka kashe da, Odo Francis Ugochukwu.

A cewar majiyar, Mutanen yankin sun haɗa kuɗi naira N230,000 cikin miliyan N10m da maharan suka buƙaci a basu.

Fulani Makiyaya Sun kashe Mutum ɗaya a Akwa Ibom

Hakanan kuma wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe, Silvanus Usen, a wani hari da suka kai Ikot Atasung dake ƙaramar hukumar Ikot Ikpene, jihar Akwa Ibom.

Wata majiya ta bayyana cewa dattawan garin ne suka hana mazauna garin kai harin ɗaukar fansa a kan makiyayan.

KARANTA ANAN: Yadda Zamu Fitar da Wanda Zai Gaje Ni a 2023, Gwamna Ganduje

Shugaban yankin, Unyime Etim, yace:

"Wanda aka kashe ɗin mafarauci ne, wanda sun saba zuwa daji su ɗana tarkon su daga baya su koma su duba."

"Da suka fita duba tarkon su da safe, sai suka ga wasu makiyaya sun saki dabobin su cikin gonakin mutane. Da suka nemi makiyayan su bar wurin, shine suka farmaki ɗaya daga cikin mafarautan kuma ya mutu nan take."

A wani labarin kuma Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa taka hoton kwankwaso da gwamna Ganduje yayi ba dagangan bane kuma ba shiryayyen abu bane, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel