Babu wasu ‘yan bindigan da suka yi sansani a Dajin Falgore na Kano - Ganduje

Babu wasu ‘yan bindigan da suka yi sansani a Dajin Falgore na Kano - Ganduje

  • Babu wasu 'yan bindiga da suka yada sansani a Dajin Falgore na jihar Kano, kamar yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya sanar
  • Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki tare da hukumomin tsaro domin karfafa ingancin tsaro a fadin jihar
  • Ya kuma bayar da tabbacin ganin cewa al'amuran tsaro ba su tabarbare a Kano kamar sauran jihohi ba

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa babu wasu ‘yan bindigan da suka kafa sansani a Dajin Falore, kamar yadda ake ta yadawa a kafafen yada labaran kasar.

Ganduje ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da sashin labarai na BBC, ya kuma kara da cewa gwamnatinsa na aiki tare da hukumomin tsaro domin karfafa ingancin tsaro a fadin jihar.

KU KARANTA KUMA: Ka fara tattara komatsanka yanzu, PDP ta aikawa gwamnan APC sakon barin kujerarsa

Babu wasu ‘yan bindigan da suka yi sansani a Dajin Falgore na Kano - Ganduje
Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce babu wasu ‘yan bindigan da suka yi sansani a Dajin Falgore na Kano Hoto: The Cable
Asali: UGC

Gwamnan Kanon ya ce matsalar rashin tsaro babban kalubale ne a kasar baki daya.

Masu kawo rahoto basu ba da rahoto daidai ba kan maganar da muka yi

Gwamna Ganduje ya kuma jadadda cewa sabanin yadda wasu kafafen yada labaran kasar suka ruwaito cewar akwai ‘yan bindiga da suka yi sansani a Dajin Falgore, ya ce ko kusa bai yi wannan furuci ba.

"Masu dauko rahoto ba su bayar da rahoto daidai ba kan maganar da muka yi. Abin da ya wakana shi ne a lokacin da aka far wa Dajin Sambisa, na gaya wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa na yi hasashe idan aka tarwatsa su a can, to za su shigo sauran dazuzzukan kasar su zauna.
"Mu kuma a jiharmu ta Kano muna da babban Dajin Falgore, sakamakon haka ina so ya ba ni dama mu yi sansanin horar da sojoji a cikin jejin.
"Mun kashe makudan kudi na biliyoyin naira a cikin jejin, kuma a yanzu haka akwai gine-gine masu yawa, kuma sojoji sun fara horar da kananan sojoji aikin harbi.
"Saboda haka abin da ya kai ni Abuja don na fadi abin da aka yi ne da kuma dalilin da ya sa aka yi shi."

Daga karshe, ya ce yana aiki sosai don ganin al'amuran tsaro ba su tabarbare a Kano kamar sauran jihohi ba.

KU KARANTA KUMA: Watanni 3 bayan sasanci, Oshiomhole ya sake komawa rikicin siyasa da Obaseki

'Yan Bindiga Sun Fara Yin Kaka-gida a Dazukan Kano, Ganduje

A baya mun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa yan bindiga sun fara mamaye dazukan jiharsa kuma akwai yiwuwar suna shirin kai hare-hare ne, Tha Nation ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne a Hedkwatar Tsaro inda ya gana da shugabannin sojoji, ya ce yan bindigan na taruwa a dajin Falgore duk da jihar na kokarin bude dazukan.

Duk da cewa ya bada tabbacin gwamnatinsa da hukumomin tsaro za su cigaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar, gwamnan yayin ganawa da babban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya roki sojojin su yi gaggawar aikin kafa sansanin horas da sojoji a dajin Falgore don sojoji su karbe dajin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel