NLC Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani Saboda Mafi Ƙarancin Albashi
- Ba'a cimma matsaya ba tsakanin gwamnatin Nasarawa da ƙungiyar kwadugo NLC reshen jihar
- Shugaban NLC na jihar Nasarawa, Yusuf Iya, yace sun yanke shawarar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani
- Ƙungiyar ta yi watsi da sanarwar gwamnatin jihar cewa ta fara aiwatar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatanta
Ƙungiyar kwadugo, NLC, ta sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani a jihar Nasarawa saboda jan ƙafa da gwamnati ke yi wajen aiwatar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata da kuma walwalarsu.
KARANTA ANAN: Yadda Zamu Fitar da Wanda Zai Gaje Ni a 2023, Gwamna Ganduje
The nation ta ruwaito cewa, NLC ta umarcin dukkan ƙungiyoyin ma'aikatan jihar da su tsunduma yajin aiki wanda aka shirya zai fara daga tsakiyar daren Talata, 15 ga watan Yuni.
An bayyana shiga yajin aikin a ranar Litinin 14 ga watan Yuni, a babban birnin jihar, Lafiya, bayan fitowa daga taron da ɓangaren zartarwa suka gudanar tare da ƙungiyoyin ƙwadugo.
Shugaban NLC na jihar, Yusuf Iya, ya bayyana wa manema labarai cewa, shiga yajin aikin ya zama wajibi saboda gazawar gwamnati wajen biya musu buƙatun su cikin wa'adin wata 2.
Yusuf Iya, yace:
"Mun baiwa wannan gwamnatin sama da shekara 2 ta yi abinda ya dace, amma sai ta dinga jan ƙafa akan lamarin."
"Kamata yayi ace mun shiga yajin aiki tun 7 ga watan Yuni, amma muka hakura sabida sarakunan mu sun saka baki."
KARANTA ANAN: Ka Shirya Wa Kawo Hari Jiharka, Wata Ƙungiya Tayi Wa Gwamna Barazana Saboda Hana Kiwo
Shugaban ya zargi gwamnati da nuna halin ko in kula wajen biya musu buƙatunsu a tarukan da suka yi, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
A cewarsa, tun da gwamnati ta gaza a dukkan ɗanar da suka bata, shiyasa suka yanke shiga yajin aiki saboda shine kaɗai gwamnati ke fahimta.
A wani labarin kuma Rundunar Soji Ta Buƙaci Ragowar Yan Boko Haram Su Miƙa Kansu Cikin Ruwan Sanyi
Sojoji sun yi kira ga ragowar yan ta'addan Boko Haram da su aje makamansu, su rungumi zaman lafiya.
GOC na runduna ta 7, A. A Eyitayo, shine yayi wannan kiran a wani taron yan jarida da sojoji suka shirya a Maiduguri.
Asali: Legit.ng