Osinbajo ya siffanta irin shugabannin da Najeriya ke bukata a kowane bangare
- Mataimakin shugaban kasar Najeriya ya bayyana irin shugabannin da Najeriya ke bukata don ci gaban kasa
- Ya ce, dole ne a samu shugabanni masu son hada kan jama'a ba masu raba su matukar ana son kasar ta ci gaba
- Ya bayyana haka ne a jihar Legas a ranar Litinin yayin wata ziyara zuwa wata fadar sarautar gargajiya a jihar
Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce Najeriya na bukatar karin shugabanni masu kwazo da shirye-shiryen hada kan kasar, Punch ta ruwaito.
Ya fadi haka ne a Legas a ranar Lahadi yayin wata ziyarar ban girma a fadar Oniru na Iruland, Oba Abdulwasiu Omogbolahan Lawal, a yayin bikin murnar nadin sarauta karo na farko.
Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai taken, ‘Najeriya na bukatar shugabannin da suke shirye domin hada kan 'yan Najeriya, in ji Osinbajo a wajen bikin cika shekara daya da nadin sarautar Oniru ’, wacce hadiminsa na yada labarai, Laolu Akande ya fitar.
KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya magantu kan batun yin ritayarsa daga siyasa
Yayin da yake yaba wa Oba saboda jagorancinsa ga mazauna Iruland wadanda suka fito daga kabilu daban-daban, Osinbajo ya ce:
“Kasarmu tana bukatar dukkan shugabanni, shugabanni mafiya kyau, shuwagabannin da suka dace, shugabannin da suka shirya hada kan kasar.
“Legas karamar zuciya ta Najeriya, kowa na nan, idan abubuwa suka yi kyau a nan, abubuwa zasu yi kyau a kasar.
Yayin da yake yi wa Oba addu’ar samun nasara a kan karagar mulki, Mataimakin Shugaban kasar ya ce ci gaban masarautarsa da jama’arta ta tabbatar da ingancin shugabancin da yake bayarwa, wanda shi ne mizani don auna matsayin sarakunan gargajiya a kasar, Channels Tv tace.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta gurgunta Najeriya, PDP ta koka kan yawan cin bashi
A wani labarin, Gwamnonin da ke karkashin jam'iyyar PDP sun hadu a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom don yin shawarwari kan yadda za a tumbuke jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2023, Premium Times ta ruwaito.
A ranar Lahadin da ta gabata ne, gwamnonin suka yi alkawarin samar da tsarin da jam'iyyar ke bukata don dawowa kan mulki a matakin tarayya a 2023.
Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya yi wannan alkawarin a wata liyafa da gwamnatin jihar Akwa-lbom ta shirya, gabanin taron kungiyar a Uyo.
Asali: Legit.ng