Ka yi zaman ka a PDP, ba mu buƙatar ka a APC, Ƙungiya ta faɗawa Gwamnan Bauchi

Ka yi zaman ka a PDP, ba mu buƙatar ka a APC, Ƙungiya ta faɗawa Gwamnan Bauchi

  • Wata kungiya na masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC a jihar Bauchi ta yi ikirarin cewa Gwamna Bala Mohammed na son komawa APC
  • Sai dai kungiyar mai suna ‘Manazarta Siyasar Jam’iyyar APC’ ta ce ba su maraba da shi a jam'iyyar na APC don haka ya cigaba da zamansa a PDP
  • A bangarenta, jam'iyyar PDP a jihar Bauchi ta bakin sakataren watsa labarai, Yayanuwa Zainabari ta karyata batun tana mai cewa mafarki kawai yan APC ke yi

Wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Bauchi, karkashin kungiyar ‘Manazarta Siyasar Jam’iyyar APC’, sun shaidawa gwamnan jihar cewa ba su da gurbinsa a jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa sun yi wannan furucin ne a matsayin martani kan jita-jitan cewa, Bala Mohammed yana shirin ficewa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya koma APC, suna mai cewa ba su maraba da shi a jam'iyyar.

Sanata Bala Mohammed
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Boko Haram: Buhari ya ƙara muku kuɗi fiye da N700bn, ba ku da sauran uzuri, Ndume ga Sojoji

Shugaban kungiyar, Yahya Idris Suleiman, wanda ya bayyan hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Litinin a Bauchi, ya ce ba su son gwamnan ya shigo APC, "domin zuwansa ba alheri bane ga jam'iyyar."

A bangarenta, jam'iyyar PDP ta yi martani ta bakin sakataren watsa labaranta, Yayanuwa Zainabari, tana mai cewa wannan jita-jitar na cewa gwamnan zai koma APC mafarki ne kawai.

Suleiman ya yi ikirarin cewa: "gwamnan yana shirin komawa jam'iyyar APC.

"Amma da izinin Allah, hakan ba zai faru ba. Ya tsaya a jam'iyyar da ta zabe shi, kada ya ci amanar PDP.

"Ya tsaya a can domin ba mu maraba da shi a jam'iyyar mu."

"Idan shi (gwamnan) yana tunanin yana aiki yadda ya kamata, mai zai sa ba zai zauna a can ba a sake zabensa idan dai da gaske yana aiki?

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Gwamnan Bauchi ya naɗa Aminu Gamawa a matsayin shugaban ma'aikatan fadarsa

"Binciken mu ya nuna cewa baya yin abin da ya dace kuma yana tara ciwo bashi masu yawa da sunan yi wa jihar Bauchi aiki," in ji Suleiman.

Suleiman ya yi kira ga yan jam'iyyar APC a jihar su kwantar da hankulansu yana mai cewa za su yi duk abin da ya dace domin hana shi dawowa APC domin su mutane masu nagarta kawai suke aiki da su.

A bangarensa, kakakin PDP, Zainabari ya ce masu ruwa da tsakin na APC ne suka kirkiro jita-jitar da nufin kawar da hankalin gwamnan daga yi wa mutane ayyuka.

Rikici Ya Barke a Wurin Taron Jam'iyyar APC a Kano

A wani labarin daban kun ji cewa an samu barƙewar rikici a wurin taron gangami na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Kano a ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Taron da ake yi a yankin Sabon Gari na jihar Kano, an shirya shi ne domin tarbar tsohon dan takarar gwamna na jam'iyyar Green Party of Nigeria, GPN, A.A. Zaura da wasu mutane da suka sauya sheka zuwa APC.

Daily Trust ta ruwaito cewa fadar da ta kaure tsakanin su ta kusa tarwatsa taron a yayin da mutane suka fara dare wa don gudun kada a raunata su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel