Da Dumi-Dumi: Rikici Ya Barke a Wurin Taron Jam'iyyar APC a Kano

Da Dumi-Dumi: Rikici Ya Barke a Wurin Taron Jam'iyyar APC a Kano

  • Rikici ya barke a wurin babban taron jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Kano
  • Rahotanni sun ce wasu daga cikin yan jam'iyyar ne suka fara dambe a yayin da ake gudanar da taron
  • Barƙewar rikicin ya saka mutane sun fara tserewa amma daga bisani an magance rikicin an cigaba da taron

An samu barƙewar rikici a wurin taron gangami na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Kano a ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Taron da ake yi a yankin Sabon Gari na jihar Kano, an shirya shi ne domin tarbar tsohon dan takarar gwamna na jam'iyyar Green Party of Nigeria, GPN, A.A. Zaura da wasu mutane da suka sauya sheka zuwa APC.

DUBA WANNAN: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

Dandazon mutane a wurin taron jam'iyyar APC a Kano
Babban taron jam'iyyar APC da aka yi a Kano. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A yayin da kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Rt Hon Hamisu Chidari ke yin jawabinsa, wasu mambobin jam'iyyar suka fara bawa hammata iska.

KU KARANTA: A karon farko, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya yi magana kan haramta Twitter a Nigeria

Daily Trust ta ruwaito cewa fadar da ta kaure tsakanin su ta kusa tarwatsa taron a yayin da mutane suka fara dare wa don gudun kada a raunata su.

Sai dai bayan ɗan wani lokaci an dakatar da faɗan kuma abubuwa sun koma yadda suke.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da abin da ya yi sanadin rikicin ba.

Daga bisani an cigaba da taron.

Rahotanni sun ce cikin wadanda suka hallarci taron domin komawa jam'iyyar na APC har da yan Kwankwasiyya wato magoya bayan tsoho gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje yana daga cikin manyan baki da suka hallarci taron na tarbar sabbin mambobin na jam'iyyar APC.

A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel