Rundunar Yan Sanda Ta Tabbatar da Mutuwar Mutum 10 a Jihar Plateau

Rundunar Yan Sanda Ta Tabbatar da Mutuwar Mutum 10 a Jihar Plateau

  • Yan sandan jihar Plateau, sun tabbatar da mutuwar mutum 10 a wani hari da yan bindiga suka kai jihar
  • Kakakin yan sandan jihar, Ubah Ogaba, yace Kwamishina ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin
  • Wani shaidan gani da ido yace ya ƙirga gawar mutum 12 a yankin da aka kai harin, da kuma wasu 5 da suka jikkata

Rundunar yan sandan jihar Plateau, tace an kashe mutum 10 a Sabon Layi dake yankin Kuru, ƙaramar hukumar Jos ta kudu, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

ASP Ubah Ogaba, kakakin hukumar yan sandan jihar, shine ya faɗi haka a wani jawabi da ya fitar ranar Litinin a Jos.

KARANTA ANAN: Ka Shirya Wa Kawo Hari Jiharka, Wata Ƙungiya Tayi Wa Gwamna Barazana Saboda Hana Kiwo

Ogaba, yace lamarin ya faru da tsakar daren ranar Lahadi, Kuma maharan sun shiga yankin a motar Hilux.

Yan sanda sun tabbatar da an kashe mutum 10 a Plateau
Rundunar Yan Sanda Ta Tabbatar da Mutuwar Mutum 10 a Jihar Plateau Hoto: thenewhumanitarian.org
Asali: UGC

Wani sashin jawabin yace:

"Mun samu rahoton kashe mutum 10 da wasu yan bindiga suka yi a Sabon Layi, Kuru, ƙaramar hukumar Jos ta kudu. Maharan sun shiga yankin a motar Hilux, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi."

"An tura jami'an yan sanda tare da sojoji yankin da lamarin ya faru. Kwamishinan yan sanda ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin, sannan kuma a kamo masu hannu a kai harin domin su fuskanci hukunci."

KARANTA ANAN: Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso

Rahoton the cable ya nuna cewa, wani shaidan gani da ido yace yan bindigan sun kashe mutum 12 yayin da wasu 5 suka jikkata.

Shaidan yace: "Na ƙidaya gawar mutum 12 a wurin da lamarin ya faru, da kuma wasu biyar da suka ji raunuka."

"A halin yanzu, waɗanda duka ji rauni suna amsar kulawa da lafiyar su a wani Asibiti da ba'a bayyana shi ba."

A wani labarin kuma Murna Ta Koma Ciki, Yadda Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefa Bam a Wurin Taron Ɗaura Aure a Jihar Neja

A wani harin bam da jirgin rundunar sojin sama ya gudanar a yankin garin Genu, jihar Neja, yayi sanadiyyar mutuwar wasu da suka halarci ɗaurin aure.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kashe yan bindiga da dama yayin wannan aiki na jirgin NAF, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel