Bayan Shafe Shekaru 12 Yana Mulki, Firaministan Israi’la Ya Rasa Ikonsa

Bayan Shafe Shekaru 12 Yana Mulki, Firaministan Israi’la Ya Rasa Ikonsa

  • Bayan shafe shekaru 12 yana cin duniyarsa da tsinke, firaministan Isra'ila ya rasa ikonsa
  • Shugaban ya shafe shekaru yana mulki kafin kasar ta sake duba ga tsarin mulkin kasar
  • Majalisar kasar ta kaddamar da zaben da ya sa shugaban ya rasa ikon nasa, yanzu ya zama shugaban adawa

Benjamin Netanyahu ya rasa ikonsa na shekaru 12 kan mulkin Isra'ila bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da sabuwar gwamnatin hadaka, BBC ta ruwaito.

Naftali Bennett na jam'iyyar Yamina zai jagoranci sabuwar "gwamnatin ta canji."

Shi zai jagoranci gamayyar jam'iyyun da suka samu rinjayen kuri'a daya wanda ya kai ga kawo karshen mulkin Netanyahu.

Mr Bennett zai zama Firaminista har zuwa watan Satumban 2023 a karkashin tsarin karba-karba.

Daga nan zai mika mulkin ga Yair Lapid, shugaban jam'iyyar Yesh Atid, na tsawon shekara biyu.

Mista Netanyahu - wanda ya fi dadewa kan mulki a kasar Isra'ila ya mamaye siyasar Isra'ila na tsawon shekaru.

KU KARANTA: Manya Na Ku Daban: Mutumin da Ya Fi Kowa Iyalai a Duniya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Natanyahu na kasar Isra'ila ya rasa ikonsa bayan shafe shekaru 12 yana mulki
Firaministan Isra'ila, Benjamin Natanyahu | Hoto: aawsat.com
Asali: UGC

A cikin jawabin da ya gabatar gabanin kada kuri'ar, Mista Bennett ya yaba da kawancen yana mai bayyana ta a matsayin muhimmiyar hanyar magance rashin daidaito.

"Mun dakatar da jirgin kasan kafin ya kai ga rami," in ji Mr. Bennett. "Lokaci ya yi da ya kamata shugabanni daban-daban, daga kowane bangare na mutane, su dakatar, su dakatar da wannan hauka." New York Times ta ruwaito.

Tuni shugaban Amurka Joe Biden ya aika da sakon taya murna ga Mista Bennett, yana mai cewa a shirye yake ya yi aiki tare da shi.

Abinda ya faru har Natanyahu ya rasa ikonsa

Mista Netanyahu ya yi wa'adin mulki sau biyar, na farko daga 1996 zuwa 1999, sannan daga 2009 zuwa 2021.

Ya kira sabon zabe a 2019 amma ya kasa yin nasarar kafa gwamnatin hadaka. Daga baya aka sake yin wasu zabuka guda biyu, wadanda dukkaninsu ba a kammala ba.

A zabe karo na uku ya haifar da gwamnatin hadin kai inda Mista Netanyahu ya amince da tsarin karba-karba ga jagoran adawa Benny Gants. Amma daga baya kawancen ya rushe a watan Disamba, ya kai ga yin zabe kawo na hudu.

Duk da jam'iyyar Likud ta Netanyahu ta samu kujeru 120 a majalisa, amma Netanyahu ya kasa kafa gwamnati, inda aikin ya koma ga Mista Lapid, wanda jam'iyyarsa ta zo na biyu da yawan kuri'u.

KU KARANTA: Abun Ban Sha’awa: Hotunan Yarinyar da Ta Fi Kowa Tsawo a Brazil Tare da Mijinta

A wani labarin, Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa Masarautar Saudiyya ta soke aikin Hajjin mahajjata daga kasashen duniya na shekarar 2021.

Shugaban na NAHCON, Zikrullah Hassan, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Fatima Usara, jami'ar hulda da jama’a ta hukumar ta fitar ranar Asabar a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Hassan ya ce NAHCON na mutunta hukuncin da Saudiyya ta yanke game da wannan batun komai tsananin hukuncin ga hukumar da kuma maniyyata a duk duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel