Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Jam'iyyar APC Biyu a Makurdi
- Yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun halaka mutum biyar a ranar Alhamis a Makurdi
- Biyu daga cikin mutanen da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin jami'an jam'iyyar APC ne
- Rundunar yan sandan jihar ta bakin mai magana da yawunta, DSP Catherine Anene ta tabbatar da afkuwar harin
Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Benue ta tabbatar da cewa jam'ianta biyu na cikin mutane biyar da wasu da ake zargin makiyaya masu kisa ne suka halaka a kauyen Zongu da ke mazabar Mbalagh a karamar hukmar Makurdi na jihar, rahoton Vanguard.
Vanguard ta ruwaito cewa yan bindigan sun tare mutanen biyar ne a safiyar ranar Alhamis a kan hanyarsu na zuwa gonakinsu suka halaka su.
DUBA WANNAN: A karon farko, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya yi magana kan haramta Twitter a Nigeria
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, Nyitamen Lorzer ya ce makiyayan sun halaka mutanen ne misalin karfe 7 na safe a wurin da suke taruwa kafin su tafi gonakinsu.
"Sun bude mana wuta sun halaka mutum biyar cikinmu. Ikon Allah ne kawai yasa ni da wani mutum guda muka tsira," in ji shi.
Sakataren rikon kwarya na jam'iyyar, Mr James Ornguga ya tabbatar da mummunan kisan yana mai cewa, 'cikin mutum biyar da aka kashe, biyu jami'an jam'iyyar mu ne daga mazabar Mbalagh.
"Mr Moses Allagh shine jami'in watsa labarai na APC a mazabar Mbalagh, yayin da Simon Ugber shine sakataren kudi," in ji shi.
KU KARANTA: Da Duminsa: NANS ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi ranar June 12, ta bayyana dalili
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue, DSP Catherine Anene ta tabbatar da cewa an kai gawarwakin mutane biyar din da suka rasu zuwa Cibiyar Lafiya na Tarayya da ke Makurdi.
A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.
Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.
Asali: Legit.ng