12 ga watan Yuni: Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga a Lagas
- Jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar June 12 a a filin shakatawa Gani Fawehinmi da ke Lagas
- Matasa dai na zanga-zangar ne domin neman a kawo karshen muguwar shugabanci da sauransu
- An damke wasu daga cikin masu zanga-zangar kafin aka sake su daga baya
'Yan sanda a Jihar Legas a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, sun harba barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zanga da suka taru a filin shakatawa Gani Fawehinmi Park domin tarwatsa su, jaridar The Nation ta ruwaito.
Filin shakatawar ya kasance matattara domin zanga-zangar ranar damokradiyya a jihar.
KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: A karshe Obasanjo ya magantu, ya bayyana kudurin dattawan kasar a taron Abuja
Sun yi gangamin ne don neman a kawo karshen mummunan shugabanci da sauransu.
Jami'an tsaron har wa yau sun kama wasu daga cikinsu kafin daga baya su sake su, shashin Hausa na BBC ta ruwaito.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya faɗa wa sashin labaran cewa 'yan sandan sun ƙuntata musu kafin sakin su.
"Na fito ne don gyaran Najeriya. Mun gaji, mun gaji da zalinci da kashe-kashe, kyakkyawar Najeriya muke nema," a cewar wani mai zanga-zanga.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fada ya kaure a tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Buhari a Abuja
Yan sanda sun damke dan jaridar Legit.ng a Abuja
A gefe guda Legit.ng ta kawo cewa jami'an yan sandan Najeriya sun damke mai daukan hoton Legit TV, Samuel Olubiyo, yayinda yake dauka rahoton zanga-zangan June12 dake gudana a birnin birnin tarayya Abuja.
Mun samu labarin cewa an dauke matashin ne yayinda yake daukan hotunan abubuwan dake gudana a filin zanga-zangan kuma aka kwace kamararsa.
Wani mai idon shaida ya bayyana mana cewa an damke Samuel ne kuma an kaishe ofishin yan sandan Apo duk da cewa ya nuna musu shi dan jarida ne.
Sai dai kuma sun sake shi daga bisani.
Asali: Legit.ng