Rashin tsaro: A karshe Obasanjo ya magantu, ya bayyana kudurin dattawan kasar a taron Abuja
- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da ya sa ba a bayyana kudurin taron dattawan kasar a Abuja, babban birnin tarayya ba ga jama'a
- Obasanjo ya ce Kwamitin Nagartar Najeriya (CGN) ya damu matuka game da matakin rashin tsaro a kasar
- A cewarsa, za a sanar da Shugaba Muhammadu a hukumance game da sakamakon taron kungiyar
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce tsofaffin shugabannin kasa karkashin inuwar kwamitin kula da nagartar Najeriya (CGN) sun sanar da Shugaba Muhammadu Buhari taron da suka yi kwanan nan a Abuja kan rashin tsaro a kasar.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasar ya ce mambobin kungiyar ta CGN sun amince bisa manufa su gabatar da kudurin su ga shugaba Buhari a hukumance kafin bayyana komai ga jama'a.
KU KARANTA KUMA: A shirye nake da na mutu domin Najeriya: muhimman batutuwa 9 da Buhari ya gabatar a jawabin ranar Demokradiyya
Legit.ng ta tattaro cewa Obasanjo ya bayar da karin haske game da abin da aka tattauna a taron su na ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, wanda a cewarsa, ya ta’allaka kan al'amuran tsaro, tattalin arziki, walwala, jin dadi, hadin kai da ci gaban Najeriya.
Obasanjo ya ce:
“Mun kunshi tsofaffin shugabannin kasa a mulkin soja da shugabannin kasa, tsohon Babban Alkalin Najeriya, da tsohon mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro. CGN ya kuma hada da kungiyoyin kwadago, ilimi, mata da sauran kungiyoyi.
"Mun amince da wasikar da aka rubuta a matsayin martani ga wasikarmu da muke sanar wa Shugaban kasa taronmu kuma sakonsa na fatan alheri shi ne cewa sakamakon taronmu zai kasance mai sha'awarsa."
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fada ya kaure a tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Buhari a Abuja
Jaridar The Guardian ta kuma ruwaito cewa tsohon shugaban kasar ya kuma lura cewa nan ba da jimawa ba ‘yan Najeriya za su fahimci dalilin haɗin gwiwar ta hanyar ayyukanta.
Obasanjo ya ci gaba da cewa:
“Matakai daga bangarenmu da na sauran mutane wadanda ake bukata nan take, za ku gansu. Munyi wa kanmu alkawarin canza labarin. Dole ne mu fara karfafa gwiwa da tuntuba. Daga yanzu, za ku ji daga matakanmu kan sakamakon tattaunawar da muka yi."
Dattawan Najeriya za su sa labule da Shugaba Buhari
A baya mun ji cewa Manyan jagororin addini a Najeriya a karkashin Sultan, Muhammad Sa’ad Abubakar III da John Cardinal Onaiyekan sun jagoranci wani zama na musamman.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa bayan kammala wannan zama da aka shafr kusan sa’o’i goma, babu wanda ya yi wa manema labarai magana a ranar Alhamis.
Punch ta ce za a dauki rahoton wannan zaama da aka yi, a kai gaban shugaba Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng