Yanzu-yanzu: Yan sanda sun damke dan jaridar Legit.ng a Abuja

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun damke dan jaridar Legit.ng a Abuja

  • Daga daukan hoton masu zanga-zanga, yan sanda na kama yan jarida
  • Bayan yan jaridan Punch da FIJ da aka fara kamawa, an damke na jaridar Legit
  • Daga baya yan sandan sun sakeshi

Jami'an yan sandan Najeriya sun damke mai daukan hoton Legit TV, Samuel Olubiyo, yayinda yake dauka rahoton zanga-zangan June12 dake gudana a birnin birnin tarayya Abuja.

Mun samu labarin cewa an dauke matashin ne yayinda yake daukan hotunan abubuwan dake gudana a filin zanga-zangan kuma aka kwace kamararsa.

Wani mai idon shaida ya bayyana mana cewa an damke Samuel ne kuma an kaishe ofishin yans andan Apo duk da cewa ya nuna musu shi dan jarida ne.

KU DUBA: A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun damke dan jaridar Legit.ng a Abuja
Yanzu-yanzu: Yan sanda sun damke dan jaridar Legit.ng a Abuja
Asali: Original

KU KARANTA: Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa

Daga baya, yan sandan sun sake shi tare da sauran jaridan da suka damke.

'Yan sanda a Jihar Legas a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, sun harba barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zanga da suka taru a filin shakatawa Gani Fawehinmi Park domin tarwatsa su.

Filin shakatawar ya kasance matattara domin zanga-zangar ranar damokradiyya a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng