Diyar biloniya Aliko Dangote ta birge masoya da takun rawanta

Diyar biloniya Aliko Dangote ta birge masoya da takun rawanta

  • ‘Yar daya daga cikin masu kudin duniya, Halima Aliko Dangote, ta birge masoya a shafin soshiyal midiya
  • Halima ta halarci wani taro sannan ta birge jama’ar da suka taru da kasaitaccen takun rawanta
  • Bidiyon ya yi fice a shafin soshiyal midiya kuma masoya sun kayatu yayinda suka bayyana ra’ayinsu game da takunta

Diyar mai kudin Najeriya, Aliko Dangote, Halima ta shiga kanen labarai kuma ta birge masu amfani da shafukan intanet.

Matashiyar matar wacce kan birge masoya da rashin hayaniyarta ta ba mutane da dama mamaki bayan ta fito ta yi rawa a wani taro da ta halarta.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yiwa babban kwamandan Agaji na kungiyar Izala ta kasa, Malam Lawan Sauri, rasuwa

Diyar biloniya Aliko Dangote ta birge masoya da takun rawanta
Halima Aliko Dangote yayinda take taka rawa a wajen wani biki Hoto: @hausaroom
Asali: Instagram

Sabanin yadda aka saba ganinta, matashiyar ta sha rawa a filin taro yayinda take rera wakar da ke tashi na shahararriyar mawakiya, Teni.

Halima ta taka rawar cikin sanyi da birgewa.

Kalli bidiyon a kasa:

Ba tare da bata lokaci ba, masoya suka yi sharhi a kan dan gajeren bidiyon nata a shafin soshiyal midiya sannan sun nuna sha’awarsu ga Halima Dangote. Karanta abunda suke fadi a kasa:

High_class_sokoto_kayan_mata:

“Tana da aji (Kana iya rawa cike da kamun kai kuma ka birge).”

Hasfin_fashion:

“Ba zan iya kirga sau nawa na kalli wannan bidiyon ba.”

Khadeejjarh:

“Masu kudi basa rawan jefa kafa.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fada ya kaure a tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Buhari a Abuja

Sameerahs_closet:

“Shakka babu ta san yadda ake takun rawa.”

Kamfanin Simintin Dangote ya yi asarar N200bn cikin kwanaki 4

A wani labarin, mun ji cewa masu hannun jari a kamfanin Simintin Dangote sun yi asara a cikin wannan makon nan yayinda arzikinsa ya samu nuksani cikin kwanaki hudu.

Masu hannun jari sun yi asarar N200 billion tsakanin Litinin da Alhamis.

Wannan ya faru ne saboda tayin wawan da yan kasuwa ke yiwa hannun jarin kamfanin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel