Kamfanin Simintin Dangote ya yi asarar N200bn cikin kwanaki 4

Kamfanin Simintin Dangote ya yi asarar N200bn cikin kwanaki 4

- Cikin kwanaki 4, an yi asarar bilyan 200 saboda masu hannun jari sun yiwa jarin kamfanin tayin wawa

- Arzikin kamfanin Simintin Dangote ya sauko daga N3.7 tr a ranar Litinin zuwa N3.5 trillion a ranar Alhamis

- Masu sanya hannun jari sun raina hannun jarin Dangote, saboda hakan masu ruwa da tsaki suka fara sayar da hannun jarinsu

Masu hannun jari a kamfanin Simintin Dangote sun yi asara a cikin wannan makon nan yayinda arzikinsa ya samu nuksani cikin kwanaki hudu.

Masu hannun jari sun yi asarar N200 billion tsakanin Litinin da Alhamis.

Wannan ya faru ne saboda tayin wawan da yan kasuwa ke yiwa hannun jarin kamfanin.

Haka ya sa arzikin kamfanin ya sauko N3.5 trillion a ranar Alhamis, daga N3.7 trillion a ranar farkon makon.

Hakan yana nufin an yi asarar akalla naira bilyan 200.

Tun ranar Talata masu sanya sannun jari suka fara rage tayin da suke yiwa hannun jarin Dangote.

DUBA NAN: Sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC ya girgiza mu kuma ya bamu kunya, Gwamnan Taraba

Kamfanin Simintin Dangote ya yi asarar N200bn cikin kwanaki 4
Kamfanin Simintin Dangote ya yi asarar N200bn cikin kwanaki 4 Hoto: @DangoteCement
Asali: Twitter

KU KARANTA: FG ta yi sulhu tsakanin Kwadago da El-Rufa'i, an yi yarjejeniya

A bangare guda, gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kudi Naira miliyan 155 ga Ma'aikatan Harkokin Addinin Musulunci na jihar domin siya wa malamai babura a jihar domin su rika yin da'awah, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Alhaji Isah Galadanci ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron Kwamitin Zartarwa na jihar a ranar Alhamis 20 ga watan Mayun shekarar 2021.

Kwamitin ta amince ta fitar da wani kudin fiye da Naira miliyan 196 domin gini da shimfida kwalta tagwayen titi mai tsawon kilomita biyar daga Achida-Tungar Malam-Lambar Kwali a ƙaramar hukumar Wurno na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel