Allah ya yiwa babban kwamandan Agaji na kungiyar Izala ta kasa, Malam Lawan Sauri, rasuwa

Allah ya yiwa babban kwamandan Agaji na kungiyar Izala ta kasa, Malam Lawan Sauri, rasuwa

  • Kwamandan kungiyar Agaji na JIBWIS ta kasa, Malam Lawan Sauri ya rasu
  • Mallam Sauri ya rasu ne sakamakon hatsarin mota a hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Juma'a, 11 ga watan Yuni
  • Za a yi jana'izarsa a babban masallacin Utako da ke Abuja a yau Asabar, 12 a watan Yuni, da misalin 1:00 na rana

Allah ya yiwa babban kwamandan Agaji na kungiyar Izala ta kasa wato JIBWIS, Malam Lawan Sauri rasuwa.

Mallam Sauri ya rasa ransa a ranar Juma’a, 11 a watan Yuni, sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da shi a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: A karshe Obasanjo ya magantu, ya bayyana kudurin dattawan kasar a taron Abuja

Allah ya yiwa babban kwamandan Agaji na kungiyar Izala ta kasa, Malam Lawan Sauri, rasuwa
Marigayi Malam Lawan Sauri Hoto: Abdullahi Bala Lau
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar Izala ta kasa, Mallam Abdullahi Bala Lau ne ya sanar da labarin mutuwar babban jami’in a shafinsa na Facebook inda yayi masa addu’an samun rahamar Allah.

Ya kuma bayyana cewa za a yi jana’izarsa a hedkwatar JIBWIS da ke babban masallacin Juma’a na Utako, Abuja a yau Asabar, 12 ga watan Yuni da misalin karfe 1:00 na rana.

Bala Lau ya bayyana Lawan a matsayin bawan Allah mai kishin addini kuma mai shiga ayyukan Da’awa tare da binsu duk wani lungu da sako na Najeriya don koyar da kalaman Allah.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fada ya kaure a tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Buhari a Abuja

Legit.ng ta tattaro martanin jama'a a kan rasuwar:

Abdulhameed Kolade Abideen-Oladimeji ya yi addu’a:

“Da fatan Allah ya karbi komawarsa, Ya gafarta masa kurakuransa ya shigar dashi Aljannarsa, Aamin.”

Muhammad Lawan Hamza ya ce:

“Da fatan Allah ya gafarta masa zunubansa baki daya, ya kare shi daga azabar kabari ya kuma ba shi Aljanna ta kasance shi ne na karshe Adobe Amin ya Rabb.”

Ibrahim Abubakar Al-ansary:

“Allah Ta'ala Ya sanya shi a jannatul furdausi.”

Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kisan Mutane 90 a sabon harin da aka kai jihar Zamfara

A wani labarin kuma, Hukumar Yan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da harin da aka kai a karamar Hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara, inda akayi asarar rayukan mutum Casa'in.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, SP Shehu Mohammed, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Gusau ranar Juma’a.

"Tabbas, zan iya tabbatar muku da cewa an kai wani hari a kauyen Kadawa da ke karamar hukumar Zurmi inda 'yan ta'adda suka bi dare wajen kai hari kan mutanen da ba'a sani ba suka kashe su cikin ruwan sanyi, ” Inji Mohammed.

Asali: Legit.ng

Online view pixel