Kimanin ‘Yan Nijeriya Miliyan 10.5m muka tsamo Daga Talauci Cikin Shekaru 2 - Shugaba Buhari

Kimanin ‘Yan Nijeriya Miliyan 10.5m muka tsamo Daga Talauci Cikin Shekaru 2 - Shugaba Buhari

  • Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace Gwamnatinsa tayi namijin kokari wajen tsamo kimanin 'yan Nijeriya Miliyan 10.5 daga halin kakanikayi
  • Ya bayyana hakkan ne a jawabin sa da ya gabatar domin zagayoywar ranar Dimokiradiyya
  • Shugaba buhari yasake jaddada kudurinsa wurin ganin cewa yan kasa sun samu ingantaccen tsaro domin samun sahihin tsarin zabe

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cire kimanin mutane miliyan 10.5 daga kangin talauci a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ya bayyana hakan ne a safiyar yau a jawabin da ya gabatar a duk fadin kasar don zagayowar Ranar Dimokiradiyya ta bana.

Shugaban ya kuma bayyana tabbacin cewa burin da ake da shi na tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci ya kai ga cin nasara.

Ya ce;

“A cikin shekaru biyu da suka gabata, mun fitar da mutane miliyan 10.5 daga kangin talauci - manoma, kananan‘ yan kasuwa, masu sana’o’i, mata yan kasuwa da makamantansu.
“Ina da yakinin cewa ana iya cimma wannan buri na cire mutane miliyan 100daga talauci kuma wannan ya bayyanar da ci gaban Rage Talauci na Kasa tare da Dabarar Ci Gaban.
“Bayanai na musamman na wannan shirin dabarun za a bayyana nan ba da jimawa ba.

KU DUBA: A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa

Shugaba Buhari
Kimanin ‘Yan Nijeriya Miliyan 10.5m muka tsamo Daga Talauci Cikin Shekaru 2 - Shugaba BuhariHoto: Aso RockVilla
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa

Shugaban ya kuma sake nanata kudurinsa na samar da yanayi mai kyau don samar da ingantaccen tsarin zabe a lokacin mulkinsa.

Sannan, ya nuna cewa ana bukatan 'yan Najeriya su bayar da tasu gudummawar ta hanyar shiga kowane mataki don tallafawa tsarin dimokiradiyya domin yi wa kowa hidima ba wai ga wani bangare ba ko kuma ga wasu' yan kalilan ba sannan su nemi amana daga shugabannin da suka zaba.

Ya kara da cewa;

"Alƙawarin da na yi na bayar da kyakyawan kula ga al'adun dimokiraɗiyya ina so ya kasance mai ɗorewa, burina na ganin an samar da adalci a tsakanin al'ummomin ƙasar har yanzu yana nan bai sauya ba kuma burina na ganin Nijeriya ta kasance ƙasa ga kowane ɗayanmu yana neman gazawa.

A bangare guda, kowane dan Najeriya ana bin sa bashin fiye da N160,000 sakamakon basukan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rika karba tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2015.

Shugaban ya ranto bashin da yawansa ya kai tiriliyan N21 ttun watan Yulin 2015, da hakan ya sanya bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan N33.1 ya zuwa watan Maris din bana, kamar yadda bayanai daga Ofishin Kula da Basukan Najeriya (DMO) suka nunar.

Bayanan basukan da gwamnatin Shugaba Buhari ta karbo idan aka fasalta shi a ko wane wayewar garin Allah Ta’ala, kasar ta rika cin bashin fiye da biliyan N10 cikin shekara shida da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel