Kaduna: Hukumar foliteknik ta Nuhu Bamalli ta rufe makarantar bayan satar dalibai da Malamai

Kaduna: Hukumar foliteknik ta Nuhu Bamalli ta rufe makarantar bayan satar dalibai da Malamai

- Hukumar makarantar Nuhu Bamalli dake Zaria a jihar Kaduna ta rufe dukkan makarantar bayan harin 'yan bindiga

- Ta sanar da hakan ne ta bakin rijistra Mahmoud Kwarbai wanda yace an yi haka ne saboda tashin hankalin da ake ciki

- A ranar Alhamis ne miyagun 'yan bindiga suka kai hari makarantar inda suka tasa keyar dalibai takwas da malamai biyu

Hukumar foliteknik ta Nuhu Bamalli dake Zaria a jihar Kaduna ta rufe dukkan makarantar har sai baba ta gani.

Ta umarci dukkan dalibai da su gaggauta barin makarantar.

Wannan ya biyo bayan harin da miyagun 'yan bindiga suka kai makarantar kuma suka sace dalibai takwas daga dakunan baccinsu tare da malami biyu daga kwatas din malaman.

KU KARANTA: APC ce za ta fitar da wanda ya gaje ni, ba ni ba, Shugaba Buhari

Kaduna: Hukumar foliteknik ta Nuhu Bamalli ta rufe makarantar bayan satar dalibai da Malamai
Kaduna: Hukumar foliteknik ta Nuhu Bamalli ta rufe makarantar bayan satar dalibai da Malamai. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Tsawon shekaru 6, mata da 'ya'yanta na kwana a bandaki bayan mijinta ya tsere

A halin harin kamar yadda Channels TV ya ruwaito, an harbe dalibi daya kuma yace ga garinku.

A wata takardar da mukaddashin rijistra na makarantar, Mahmoud Kwarbai ya fitar a ranar Juma'a, ya ce hukumar tace wannan matakin an dauke shi ne sakamakon tashin hankalin da harin ya janyo tsakanin daliban.

Amma kuma wannan umarnin bai shafi daliban da zasu fara rubuta jarabawar IJMB ba a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a ranar Talata, 15 ga watan Yuni.

Daily Trust ta ruwaito yadda miyagun 'yan bindiga suka kutsa makarantar har zuwa kwatas din malamai da dakunan kwanan dalibai kuma suka sace su.

A wani labari na daban, fitacce kuma jarumin mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari ya bayyana yadda ya samu barazana sama da 100 daga Boko Haram, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami.

A wata takardar da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni kuma legit.ng ta gani, babban dan sandan yace babu wata barazana da za ta hana shi da rundunar shi baiwa 'yan Najeriya kariya.

Ya kara da cewa dukkan hukumomin tsaron kasar nan ba zasu yi kasa a guiwa ba wurin yaki da ta'addanci. Ya tabbatar da cewa dukkan 'yan ta'adda da makasa da ke fadin kasar nan sai sun ji kunya da izinin Ubangiji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: