APC ce za ta fitar da wanda ya gaje ni, ba ni ba, Shugaba Buhari

APC ce za ta fitar da wanda ya gaje ni, ba ni ba, Shugaba Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace jam'iyya mai mulki ta APC ce za ta yanke hukunci kan wanda zai gaji kujerarsa

- Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa ta musamman da aka yi da shi inda aka tambayeshi wanda zai gaje shi

- A cewar shugaban kasan abinda kawai mulkin nan zai iya shine tabbatar da cigaban rinjayen jam'iyyar APC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace jam'iyyar APC mai mulki ce zata yanke hukuncin wanda wanda zai gaje shi ba wai shi da kansa ba.

Ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Arise Tv yayin wata tattaunawa ta musamman, Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaban kasan ya ce, "A kan wanda ya gajeni, abinda wannan mulkin zai iya shine ya tabbatar da karkon APC har bayan saukarmu.

KU KARANTA: Da duminsa: Twitter ta garzaya wurin FG domin neman sasanci

APC ce za ta fitar da wanda ya gaje ni, ba ni ba, Shugaba Buhari
APC ce za ta fitar da wanda ya gaje ni, ba ni ba, Shugaba Buhari. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Jami'an EFCC sun yi wa shugaban NBA na Makurdi mugun duka, yana kwance a asibiti

"Mun fara rijista daga gunduma zuwa karamar hukuma zuwa matakin jiha. Ta wannan hanyar ne APC za ta san yawan mambobinta na jiha da jiha da kananan hukumomi. Ta hakan kuma idan muka sauka, za ta cigaba da mulki.

"Wannan ce hanya mafi kyau da jam'iyya zata cigaba kuma kasa ta cigaba."

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, shugaban kasan yace masu rike da mulkin jam'iyyar na rikon kwarya na aiki babu kakkautawa wurin gyaran jam'iyyar tare da karbar kowanne dan jam'iyyar.

Buhari ya ce, "Manufar wannan mulkin shine ganin APc ta daure har a gaba. Don haka mu bar jam'iyyar ta yanke hukunci.

"Ba zata zauna a nan Legas ba, a misali kuma kana yanke hukuncin makomar APC. An fara gyaran jam'iyyar tun daga matakin kasa da rijistar kowanne dan jam'iyya. Dole ne kowanne dan jam'iyyar ya shiga.

"Nan babu dadewa za mu yi gagarumin taron jam'iyyar. Babu dan jam'iyya daya da zamu bari ya baude daga manufar jam'iyyar."

A wani labari na daban, Samuel Ortom, gwamnan jihar Binuwai, ya ce dakatar da Twitter hanya ce ta kawar da hankulan 'yan Najeriya wacce gwamnatin tarayya ta samo domin rufe gazawarta a fannin shawo kan rashin tsaro.

A wata wallafa da yayi a Twitter a ranar Talata, Ortom yace dakatarwan an yi ta ba bisa ka'ida ba inda ya kwatanta lamarin da takura tare da danne hakkin 'yan Najeriya.

Gwamnan jihar Binuwai din ya kara da cewa wannan abu da gwamnati tayi wata hanya ce ta toshe kafafen sada zumuntar zamani, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel