Tsawon shekaru 6, mata da 'ya'yanta na kwana a bandaki bayan mijinta ya tsere

Tsawon shekaru 6, mata da 'ya'yanta na kwana a bandaki bayan mijinta ya tsere

- Wata mata da 'ya'yanta sun gigita kafar sada zumunta bayan bidiyonsu ya bayyana inda suke kwana a bandaki

- Matar da 'ya'yanta sun fara rayuwa a bandaki ne bayan mijinta ya gudu daga inda suke rayuwa tare da yin watsi dasu

- Kamar yadda matar ta sanar, mai gidan da suke haya ya koresu daga gidan saboda sun kasa biyansa kudin haya

Bidiyon wata mata da 'ya'yanta dake rayuwa a bandaki na tsawon shekaru shida ya bayyana a kafar sada zumunta.

A wani bidiyo da @afrimax_tv ta wallafa a Instagram, matar ta ce rayuwar da suke ciki ita ake kira da kangi. Ita da yaranta sun taba rayuwa mai dadi amma yanzu rayuwar ta musu daci.

KU KARANTA: Jami'an EFCC sun yi wa shugaban NBA na Makurdi mugun duka, yana kwance a asibiti

Tsawon shekaru 6, mata da 'ya'yanta na kwana a bandaki bayan mijinta ya tsere
Matar da 'ya'yanta sun kwashe shekaru 6 suna kwana a tsohon bandaki. Hoto daga @afrimax_tv
Asali: Instagram

KU KARANTA: Bidiyon mahaifin amarya yana kwasar rawa a liyafa, baki sun matukar shan mamaki

Kamar yadda matar tace, mijinta a da mai kula ne kuma suna rayuwarsu mai dadi cike da farin ciki. Amma kwatsam ya canza inda ya koma dan giya.

Yana komawa gida a bige, ya daki matarsa da 'ya'yansa. Kowa ya san yadda suke buga dambe a kowacce rana.

Kwatsam wata rana mutumin ya tashi ya sanar da iyalansa cewa zai tafi wani wuri mai nisa. Basu sake ganinsa ba daga nan.

Bayan sun yi watanni shida a gidan da suke haya, an koresu saboda sun kasa biyan kudin haya. Matar bata da kawaye ko 'yan uwa da zasu iya taimakonsa, don haka suka shiga titi ita da 'ya'yanta inda daga bisani suka samu wani tsohon bandaki suna kwana.

Ga martanin jama'a:

@harrisonntaylor ya rubuta: "Yanzu yaran sai su girma kuma su zama mutane kawai wani sai ya bayyana a matsayin mahaifinsu yana neman yafiya. Ni sai dai in kira kwarankwatsa ta gama da mutum."

@emereujunwa6 ya ce: "Nagodewa Ubangiji da abinda ya bani a yau kuma ina fatan ya baiwa wadanda ke fama a koda yaushe."

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace jam'iyyar APC mai mulki ce zata yanke hukuncin wanda wanda zai gaje shi ba wai shi da kansa ba.

Ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Arise Tv yayin wata tattaunawa ta musamman, Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaban kasan ya ce, "A kan wanda ya gajeni, abinda wannan mulkin zai iya shine ya tabbatar da karkon APC har bayan saukarmu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng