Boko Haram da 'yan bindiga sun yi min barazana sama da sau 100, DCP Abba Kyari

Boko Haram da 'yan bindiga sun yi min barazana sama da sau 100, DCP Abba Kyari

- DCP Abba Kyari ya sha alwashin shi da rundunarsa ba zasu sassauta ba wurin yaki da ta'addanci a Najeriya ba

- Kyari ya sha wannan alwashin a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni a wata wallafar da yayi na cewa babu barazanar da za ta hana shi aiki

- Kamar yadda yace, rundunarsa na cafke 'yan Boko haram da sauran miyagu a kasar nan ba tare da duban kabila ko addini ba

Fitacce kuma jarumin mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari ya bayyana yadda ya samu barazana sama da 100 daga Boko Haram, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami.

A wata takardar da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni kuma legit.ng ta gani, babban dan sandan yace babu wata barazana da za ta hana shi da rundunar shi baiwa 'yan Najeriya kariya.

KU KARANTA: Bidiyon mahaifin amarya yana kwasar rawa a liyafa, baki sun matukar shan mamaki

Boko Haram da 'yan bindiga sun yi min barazana sama da sau 100, DCP Abba Kyari
Abba Kyari yayi bayanin yadda 'yan Boko Haram da 'yan bindiga ke barazanar kai shi lahira. Hoto daga Abba Kyari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Arziki: Floyd May-weather ya bayyana da agogon N8.9 biliyan, jama'a sun gigice

Ba zamu yi kasa a guiwa ba wurin yaki da ta'addanci a Najeriya ba

Ya kara da cewa dukkan hukumomin tsaron kasar nan ba zasu yi kasa a guiwa ba wurin yaki da ta'addanci. Ya tabbatar da cewa dukkan 'yan ta'adda da makasa dake fadin kasar nan sai sun ji kunya da izinin Ubangiji.

Kyari ya ce: "Na samu barazana sama da 100 daga 'yan Boko Haram, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane, 'yan fashi da makami da sauran 'yan ta'adda. Mun yi rantsuwar baiwa kasarmu kariya daga dukkan sharri. Ba zamu yi kasa a guiwa ba.

"Boko Haram, 'yan bindiga, IPOB, 'yan daba da masu tausaya musu zasu iya cigaba da bata lokacinsu da barazana, ba za ta yi aiki ba."

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace jam'iyyar APC mai mulki ce zata yanke hukuncin wanda wanda zai gaje shi ba wai shi da kansa ba.

Ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Arise Tv yayin wata tattaunawa ta musamman, Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaban kasan ya ce, "A kan wanda ya gajeni, abinda wannan mulkin zai iya shine ya tabbatar da karkon APC har bayan saukarmu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel