Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Sheƙe Sufetan Ofishin

Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Sheƙe Sufetan Ofishin

  • Wasu yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda inda suka hallaka sufetan yankin
  • Rahotanni sun bayyana cewa an yi musayar wuta tsakanin jami'an yan sanda da kuma maharan
  • Kakakin yan sandan jihar Anambra, yace ba ya son magana akan lamarin har sai yaje ya gane wa idon sa

Wasu yan bindiga aƙalla 15 sun kai hari ofishin yan sanda dake Ojoto, karamar hukumar Idemili ta kudu, jihar Anambra, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Sake Bada Umarnin Harbi Akan Duk Wanda Aka Kama da AK-47

Rahotan Thisdaylive ya bayyana cewa maharan sun hallaka sufetan caji ofis ɗin a yayin harin.

Wata majiya a yankin da abun ya faru ta bayyana cewa jami'an tsaron dake bakin aiki sun maida martani ga yan bindigan, inda akai ɗauki ba daɗi tsakaninsu.

Yan Bindiga
Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Sheƙe Sufetan Ofishin Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

"Yan bindigan na zuwa suka buɗe wuta amma jami'an yan sanda suka maida martani, maharam sun zo a motar Sienna guda biyu." inji majiyar.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, yace bayason magana akan lamarin har sai bayan ya ziyarci ofishin.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa

"Ina shirin zuwa wurin, a halin yanzun ba zance komai har sai bayan naje wurin da abun ya faru." inji Tochukwu.

Amma wani babban jami'in ɗan sanda a jihar wanda ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da kai harin.

Yace: "An kashe mana sufetan yanki yau. Kwamishinan yan sanda, Chris Owolabi, ya shirya kai ziyara yankin."

A wani labarin kuma Yaƙi da Cin Hanci a Mulkin Demokaraɗiyya Yana da Matuƙar Wahala, Buhari

Shugaba Buhari ya koka da wahalar yaƙi da cin hanci da rashawa a mulkin demokaraɗiyya, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Shugaban yace tun sanda aka zaɓe shi a matsayin shugaba shekara 6 da ta wuce yake shan wahala wajen yaƙar masu cin hanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel