Makinde: A bamu dama mu damka wa 'yan bangan Amotekun bindigar AK-47

Makinde: A bamu dama mu damka wa 'yan bangan Amotekun bindigar AK-47

- Gwamnan jihar Oyo ya bayyana aniyarsa ta sayawa 'yan bangan Amotekum bindigu AK-47

- A cewarsa, hakan zai inganta tsaro a yankin matuka ganin ingancin aikin 'yan bangan na Amotekun

- Ya ce zai nemi gwamnatin tarayya ta ba Amotekun lasisin rike bindigogi AK-47 a fadin yankin

Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, ya ce idan doka ta yarda, zai gwammace jami'an bangan Amotekun, su dauki bindigogin AK-47 don bunkasa ayyukan tsaro, The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya fadi haka ne a jawabin da ya gabatar a garin Ibadan ranar Talata a wajen bude taron dimokiradiyya na kasa mai taken, "Makomar dimokuradiyya a Najeriya."

Gwamnan ya ce nasarorin da kungiyar ta samu ya zuwa yanzu ya samo asali ne daga tsarin daukar ma'aikata wanda ya tabbatar da cewa an zabi masu gudanar da aikin daga manyan hukumominsu.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun lalata sansanin IPOB a Imo, sun ceto wata, sun kwato bindigogi

Makinde: Idan muka samu dama zamu saya wa 'yan bangan Amotekun bindiga AK-47
Makinde: Idan muka samu dama zamu saya wa 'yan bangan Amotekun bindiga AK-47 Hoto: topnaija.ng
Asali: UGC

A cewarsa, da an magance matsalolin da kasar ke fuskanta, idan aka ba gwamnatocin jihohi ikon kula da jami'an tsaro a jihohinsu.

Jaridar Punch ta rahoto in da gwaman ke cewa:

“Eh, za mu ci gaba da yin iya kokarinmu. Mun sami damar ciro Amotekun daga kasa kuma tana aiki yanzu… amma akwai iyakoki da yawa ga abin da Amotekun zasu iya yi a yanzu da nau'ikan bindigogin da za su iya rikewa. Idan aka bamu iko da lasisi, ni kuma zan sayi bindigogin AK47 ga Amotekun.

KU KARANTA: Jami'ar Najeriya ta kera maganin Korona, saura kiris a sake shi

A wani labarin, Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya ce gwamnatinsa za ta karfafa cin naman alade a madadin naman shanu don tattala miliyoyin nairorin da jihar ke asara ga sauran jihohin da ke samar da naman shanu da sauran nau'ikan nama, Daily Trust ta ruwaito.

Akeredolu ya fadi haka ne a ranar Litinin yayin kaddamar da wani babban mayankar alade ta Dutchman Piggery da kayan tallafi a Ilutoro da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar a matsayin wani bangare na ayyukan cikarsa kwanaki 100 a ofis.

A cewar gwamnan, kudin da ake kashewa ga wasu jihohin da ke samar da shanu da sauran nau'ikan nama zasu kasance a jihar don kara tattalin arzikin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: