Yan Majalisar Wakilai Sun Buƙaci Shugaban Hukumar FIRS Yayi Murabus Daga Muƙaminsa

Yan Majalisar Wakilai Sun Buƙaci Shugaban Hukumar FIRS Yayi Murabus Daga Muƙaminsa

- Kwamitin dake kula da asusun fili na gwamnati a majalisar wakilai ta ƙasa yayi kira ga shugaban FIRS yayi murabus

- Kwamitin ya nuna matukar damuwarsa bisa ƙin halartar gayyatar da aka masa don ya amsa tambayoyi.

- Amma wakilin shugaban FIRS, Mr Olusegun Olatunji, ya bada hakuri a madadin shugabansa

Kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar wakilai yayi kira ga shugaban hukumar karɓar haraji ta ƙasa (FIRS), Muhammad Nami, yayi murabus daga muƙaminsa nan take idan bazai iya sauke nauyin da aka ɗora masa ba.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Bayan Kamfanin Twitter Ya Nemi Sasanci, FG Ta Kafa Masa Sabon Sharadi

Kwamitin ya nuna rashin jin daɗinsa game da shugaban FIRS saboda rashin amsa gayyatar da aka masa domin jin ta bakinsa a Ranar Laraba.

Sai-dai kwamitin ya sake aikewa Muhammad Nami da buƙatar ya bayyana a gabanshi gobe Alhamis, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Badaƙalar Kuɗin Haraji: Yan Majalisa Sun Nemi Shugaban FIRS Yayi Murabus
Badaƙalar Kuɗin Haraji: Yan Majalisa Sun Nemi Shugaban FIRS Yayi Murabus Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yan majalisar wakilai sun fara bincikar Ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya bisa zargin wata badaƙala da aka tafka kan tattara kuɗin haraji.

An gayyaci shugaban hukumar FIRS ya bayyana gaban kwamitin domin yayi ƙarin haske kan dalilin da yasa wasu kamfanonin waje ba su biya kuɗin haraji ba.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Magana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield

Mataimakin shugaban kwamitin, Abdullahi Abdulƙadir, ya nuna bacin ransa bisa rashin zuwan shugaban FIRS a wannan taro mai matuƙar muhimmanci.

Wakilin shugaban FIRS, Mr Olusegun Olatunji, ya baiwa yan majalisar wakilan hakuri a madadin Mr. Nami, sannan ya alaƙanta rashin zuwan shugabansa da cewa bai samu saƙon gayyatar kwamitin da wuri ba.

A wani labarin kuma Har Yanzun Babu Jam'iyyar Siyasa Kamar PDP a Nahiyar Africa, Secondus

Uche Secondus, shugaban PDP na ƙasa, yayi iƙirarin cewa babu wata jam'iyyar siyasa kamae PDP a Africa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Secondus ya faɗi haka ne a sakateriyar jam'iyyar na ƙasa dake Abuja , yayin kaddamar da kwamitin rijista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel