Sojoji Sun Aike Da 'Yan Boko Haram Shida Lahira a Jihar Borno
- Dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP da dama a Dikwa dake jihar Borno
- Maharan sunyi yunkurin afkawa garin ne a ranar Talata, cikin zafin-nama sojojin suka hau ragargazarsu
- Kakakin rundunar sojin, Mohammed Yerima ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba
Dakarun sojin Najeriya sunyi nasarar ragargazar ‘yan ta’addan ISWAP a Dikwa, jihar Borno, The Punch ta ruwaito.
The Cable ta ruwaito cewa maharan sunyi yunkurin kai farmaki yankin ne a ranar Talata, cikin kankanin lokaci sojoji suka far musu da harbe-harbe.
Kakakin rundunar sojin, Mohammed Yerima ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba wacce ta bayyana yadda ‘yanta’addan suka isa garin da miyagun makamai, yayin da wasunsu suka shiga Dikwa ta wuraren Gajibo a baburansu.
DUBA WANNAN: Matar El-Rufai: A Shirye Nake In Mutu Hannun Masu Garkuwa, Kada a Biya Kuɗin Fansa Idan An Sace Ni
“Sunyi kacibus da manyan dakarun rundunar sojin sama,” a cewarsa.
“Sojojin sunyi kaca-kaca dasu sun kuma rikitar da tunaninsu matuka yayin da suka kwace duk wasu makamansu.
“Sakamakon batakashin da akayi, an samu nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama yayin da wasu suka samu miyagun raunuka, sauran da suka rage kuwa sun tsere cikin hanzari inda suka bar gawawwakin abokan harkarsu.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Majalisa Za Ta Tantace Hadimar Buhari Da Wasu Mutum 5 a Matsayin Kwamishinoni a INEC
“A cikin abubuwan da aka kwace a hannunsu akwai motar yaki, bindigogi kirar AK 47 guda 8, babura 3, magazin 6 da sauran manyan miyagun makamai.
“Don tabbatar da tsaron yankin, saida rundunar soji tayi asubanci tare da ‘yan sakai da mafarauta inda su zagaye garin da kewaye har suna tsintar wasu makamar da ‘yan bindigar suka tsere suka bari."
Saidai ya bayyana yadda sojoji 3 suka raunana amma yanzu haka ana kulawa da lafiyarsu a Dikwa.
Ya kara da bayyana yadda shugaban rundunar sojin Najeriya, Faruk Yahaya ya yabawa sojojin bisa jajircewa da dagewarsu.
A wani rahoton daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.
Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.
Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.
Asali: Legit.ng