Har Yanzun Babu Jam'iyyar Siyasa Kamar PDP a Nahiyar Africa, Secondus

Har Yanzun Babu Jam'iyyar Siyasa Kamar PDP a Nahiyar Africa, Secondus

- Uche Secondus, shugaban PDP na ƙasa, yayi iƙirarin cewa babu wata jam'iyyar siyasa kamae PDP a Africa

- Secondus ya faɗi haka ne a sakateriyar jam'iyyar na ƙasa dake Abuja, yayin kaddamar da kwamitin rijista

- Yace muna faɗin haka ne ba wai ɗan alfahari ba, sai don mun san hakan shine zahiri

Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Uche Secondus, yace kasancewar jam'iyyar su na ɓangaren adawa, hakan bai rage mata girmanta na babbar jam'iyya a Nahiyar Africa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Bayan Kamfanin Twitter Ya Nemi Sasanci, FG Ta Kafa Masa Sabon Sharadi

Shugaban ya faɗi haka ne ranar Laraba, a wajen ƙaddamar da kwamitin yin rijistar zama ɗan jam'iyya ta yanar gizo a sakateriyar jam'iyyar dake Abuja.

Secondus yace duk da APC ta ɗare kan karagar mulki na tsawon shekara 6, amma har yanzun ba ta kama kafar ƙarfin da PDP ke da shi ba faɗin ƙasar nan ba.

Har Yanzun Babu Jam'iyyar Siyasa Kamar PDP a Nahiyar Africa, Secondus
Har Yanzun Babu Jam'iyyar Siyasa Kamar PDP a Nahiyar Africa, Secondus Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shugaban yace: "Idan mukace babu wata jam'iyya kamar PDP a dukkan ƙasashen nahiyar Africa, ba wai mun kuranta ta bane, muna faɗin abinda ke zahiri ne."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Magana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield

"A zaɓen 2019, jam'iyyar PDP ita kaɗai ce ta tsayar da yan takara a kowace kujera kuma a kowane mataki na gwamnati, zaɓen shugaban ƙasa, gwamnoni, sanatoci, yan majalisar wakilai da kuma yan majalisar dokokin jihohi 36 da muke da su."

"Har a jihohin da ba ɗan jam'iyyar mu ne a kan mulki ba, mambobin mu sun fito an fafata da su."

A wani labarin kuma Mun Shiga Ƙuncin Rayuwa Saboda Tsare Mahaifanmu, 'Ya'yan El-Zakzaky Sun Koka Ga Buhari

Iyalan Sheikh Ibrahim El-zakzaky, shugaban ƙungiyar mabiya shi'a IMN, sun bayyana irin halin da suke ciki na rashin iyayen su

Ɗaya daga cikin yayan malamin, Suhaila Ibrahim, ita ce ta faɗi haka a wata fira da tayi da kafar watsa labarai ta BBC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262