Da Dumi-Dumi: Bayan Kamfanin Twitter Ya Nemi Sasanci, FG Ta Kafa Masa Sabon Sharadi

Da Dumi-Dumi: Bayan Kamfanin Twitter Ya Nemi Sasanci, FG Ta Kafa Masa Sabon Sharadi

- Kamfanin twitter ya garzaya wurin gwamnatin tarayya domin a zauna teburin tattaunawa

- Rahotanni sun bayyana cewa Kamfanin na asarar maƙudan kuɗaɗe saboda matakin hana anfani da shafin da FG ta ɗauka

- Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, yace ya zama wajibi kamfanin yayi rijista a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kamfanin twitter ya tuntuɓeta domin sasanci dangane da matakin da gwamnatin ta ɗauka na hana amfani da shafin.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Magana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwar ta tarayya.

Taron wanda ya gudana a gidan gwamnatin tarayya dake Abuja, shugaba Buhari ne ya jagorance shi, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Da Dumi-Dumi: Bayan Kamfanin Twitter Ya Nemi Sasanci, FG Ta Kafa Masa Sabon Sharadi
Da Dumi-Dumi: Bayan Kamfanin Twitter Ya Nemi Sasanci, FG Ta Kafa Masa Sabon Sharadi Hoto: dw.com
Asali: UGC

Ministan yace ya zama wajibi twitter yayi rijista a matsayin kamfanin kasuwanci a Najeriya, ya ƙara da cewa wannan ne sharaɗin da dole zai ciƙa kafin a ɗage dokar hana hawa shafin.

KARANTA ANAN: FG Ta Fito da Wani Sabon Tsari, Zata Tallafawa Yan Najeriya Miliyan Ɗaya da N5,000 na Tsawon Wata 6

Mr. Muhammed yace sauran kafafen sada zumunta kamar Facebook da Instagram, suma dole sai sun yi rijista a Najeriya, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Muhammed yace dakatar da twitter ya zama wajibi saboda dandalin ya samar da wata kafa ga waɗanda suke barazana ne ga zaman Najeriya ɗaya.

Yace shafin twitter ya bar shugaban yan taware IPOB, Nnamdi Kanu, yayi amfani da dandalin wajen kira da a kashe jami'an yan sanda.

Yace kamfanin yaƙi ya goge rubutun duk da neman yayi hakan da gwamnati tayi ba sau ɗaya ba.

A wani labarin kuma FG Ta Yi Ƙarin Haske Kan N-Power, Tace Mutum 550,000 Ne Suka Tsallake Matakin Tantancewa

Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan matakin da ake na ɗaukar ma'aikata a shirin N-Power, kamar yadda vanguard ya ruwaito.

Ministan Ma'aikayar jin ƙai da walwala, Sadiya Farouq, ita ce tayi jawabi dangane da shirin yau a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel